Spread the love

Gidauniyar Dangote ta tallafawa mata sama da dubu 23 a jihar Sakkwato

Gidauniya Aliko Daangote ta bayar da tallafin kudi ga mata dubu 23,990 kimanin  kudi miliyan 239.9 kowace mace za ta amfana da dubu 10 a fadin jihar Sokoto.

Shugaban Gidauniyar Alhaji Aliko Dangote ya ce wannan tallafin yana cikin shirinsa na tallafawa masu karamin karfi.

Dangote ya ce a watan azumin bara ma Gidauniyarsa ta tallafawa masu karamin karfi  dubu 106 a jihohin Sokoto da Katsina Kebbi da Zamfara da abinci da yawan kudin suka kai miliyan 300.

Ya ce cigaba da tallafin ne ya sanya suke a Sokoto domin kaddamar da mataki na biyu na tallafi matsakaici ga  masu karamin karfi.

‘A sokoto za mu bayar da tallafi ga mata dubu 23,990 da kuma mata ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Rabah da yawansu ya kai  990. Matan mabukata da hukumar zakka ta tance su za a ba kowacensu duba 10, su yi jarin duk sana’ar da suke so. Hakan na iya tabbata in suka yi sana’a za su samar da wasu kudin shiga a gidajensu za su rage radadin talauci dake addabar rayuawarsu’ a cewarsa.

Ya nuna gamsuwarsa ga hukumar Zakka da wakafi da alkawalin cigaba yin hadaka da hukumar domin taimakawa maras karfi. Ya ba da sanarwar ba da wasu miliyan 80 ga hukumar domin cigaba da shirinta na baiwa masu karamin karfi bashin da bai da ruwa in da suke da kudi miliyan 21.1 don soma shirin.

Shugaban hukumar Zakka da wakafi Malam Muhammad Lawal Maidoki ya godewa hamshakin dan kasuwar da wannan hobbasar in da ya yi fatan sauran ‘yan kasuwa da attajiran kasar nan su yi koyi da shi domin alfanun da take cikin taimakon mara karfi da ma bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *