ZAN IYA YIN AMFAMI DA YAREN COMPUTER A WAYAKA TA ANDROID(Computer programing language)

Da yawa daga cikin mutanenmu suna da niyya da kuma zummar koyon programming, amma babban abin ke kawo musu cikas shine rashin kwamfuta. Mafi yawncin mutane suna ganin cewa indai baka mallaki kwamfuta ba to babu ta yadda zaka yi ka koyi programming. To a halin yanzu wannan magana zamu iya cewa ba haka take ba, domin a wannan zamanin da muke ciki ko da waya ma zaka iya koyo da kuma kwarewa akan programming, kamar yadda zaku gani a cikin wannan rubutun nawa.
Sanin kowa ne dai shigowar waya kirar Android, shekaru da suka gabata, kawo yanzu an samar ci gaba da dama, ta yadda akwai Applications da dama wadanda sanin kowa ne a baya ba zaka iya saminsu ba akan wayoyin hannu sai dai akan kwamfuta, to amma yanzu abu ne mai sauki samin wadannan application a saman wayoyinmu. Yanzu har ma takai wasu applications din ma na Android kadai zaka iya samu amma ba zaka sami na kwamfuta ba.
A cikin bangarori da dama da suka samu habbaka sanadiyyar shigowar wayar Android akwai bangaren programming. A halin da muke ciki yanzu, kusan ko wane irin programming da ka sani zaka iya samin application din ake amfani wajen yinshi a dandalin applications na android wato Google Play store. Dukkan manya-manyan programming da ka sani kama daga Java, C, C++, HTML, PHP, CSS, da dai sauransu duk zaka iya samun apps din da zaka iya amfani da shi wajen programming a saman google play, kuma duk kwautane. Kai har ma da application din ake amfani da shi wajen hada android apps (wato AIDE) duk zaka iya samu a can.
Kaga ke nan bai kamata ka rika kyamar programming ba kawai don baka da kwamfuta. Indai har kasan akwai wani programming din kake son koyo kawai abin da zaka yi shine ka garzaya a Google Play Store domin ka binciko application din da zaka yi amfani da shi domin yin wannan programming din. kuma wani abin farin ciki ma shine kusan dukkan wadannan applications din kyauta ne wato baka bukatar biyan ko kobo domin yin amfani dasu, sai data Kawai da zaka dauko su zuwa wayanka.
Domin tambaya ko kuma neman karin bayani za turo sako 08142670616. 2 A shirye nake na amsa dukkan tambayoyinku. Daga baya za a turoma da sakon links da zaka Ga ansar tambayarka a shafinan namu ta sakon waya.
Shafiu( Garba Shahf) sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *