Spread the love

A ranar Lahadi aka samu wata hatsaniya tsakanin sojojin sama da matasan unguwar Maberar Fulani a jihar Sakkwato kan zargin wai sun yi wa wata budurwar Soja abin da bai da ce ba.

Hatsaniyar ta kai ga rasa rayuwar matar gida Maryam Abdurrahaman ‘yar shekara 40 dake da ‘ya’ya bakwai maza da mata da wani matashi dan shekara 23 Abdulsalam lawal dan makaranta, aka jikkata wasu mutum shidda maza cikinsu akwai wanda ya karye a hannu sauran suka samu rauni a kafafunsu.

Abdurrahaman Hassan kane ne ga margayiya da sojojin suka harba ya ce a Lahadi ne babban danta Ahmad ya kira shi a waya ke fada mashi sojoji sun harbe mahaifiyarsa saboda wasu matasa da yarinyar soja ne suka yi hatsaniya ta kirawo su suka rika baiwa mutane kashi har abin ya koma fada suka harbi mutane abin ya shafeta tana cikin gida, an kaita asibiti ana duba ta namijin da aka harba a ciki hanjinsa sun fito ya rasu daga nan ita kuma ta bar duniya, akwai matar da aka buga da bindiga. Muna kira ga gwamnati ta kwato mana hakkinmu an zulunce mu da ‘ya’yan wannan matar.

Muhammad Mai yadi dake unguwar ya nemi gwamnati ta kwato masu hakkinsu a yi adalci kan lamarin duk mai gaskiya a bashi gaskiyarsa matukar ana son zaman lafiya.

Tun da lamarin ya faru al’ummar jihar Sokoto ke ta alawadai da lamarin da fatan gwamnati za ta shiga lamarin domin bai kamata ta rika kallo ana cin zarafinsu ba.

A duk in da ka ga mutane a zaune matukar sun dauko maganar sai sun yi tir da wannan halin dabbobi da wadan nan sojoji suka yi ga farar hula kan macen da ake zargin budurwar wani daga cikinsu ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *