Spread the love

Matar Gwamnan jihar Kebbi Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta yi wani dogon bayani ga mutanen Nijeriya kan abin da ya shafi gidauniyarta da siyasar jihar Kebbi da halin mijinta Sanata Atiku Bagudu.

Dakta ta ce kuɗin da take ta fiyar da gidauniyarta ta kula da ciwon daji ma’ana kansa tana samunsu ne a tallafin ƙungiyoyin duniya da rigunan gidauniyar da suke sayarwa, gwamnati da wasu ɗaiɗaikun jama’a suna saye don ƙara ƙarfafa gidauniyar.

Ta ce Duk abin da suke yi yana cikin zauren bayanansu a yanar gizo yana da kyau mutum ya shiga ya bincika ba wai ya riƙa shiga kafofin sada zumunta yana ƙoƙarin cin zarafin aikin da ake yi ba.

Kan maganar ƙananan hukumomi sun tarawa gidauniyarta kuɗi ta ce ‘wannan ba gaskiya ba ne ƙarya ce aka riƙa yawo da ita ban san da wannan maganar ba ba a yi ta ba.”

Ta ƙara da cewar da zaran an ga mun yi wani abu a gidauniyarmu sai ɗauka da kuɗin jihar Kebbi ne wanda ba haka ba ne mijinta mutum ne mai amana ba ya yarda a ci kuɗin jiha ba da haƙƙi ba.

“dubi yanda ya inganta albashin likitocin adibiti ya gyara Birnin Kebbi yanzu sai a yi ruwa ba ambaliya, manoma na yi masa sambarka yadda ya kula da su” in ji Zainab.

Ta ce gidauniyarta ba ta ‘yan jihar Kebbi da Zamfara ba ce duk wata mai matsalar kansa a Nijeriya za ta taimaka mata matuƙar ta sameta.

Ta yanke shawarar ɗaukar ciwon ne domin shi ne wanda yafi matsala warkewa in ka dubi irinsu maleriya wanda za ka iya warkewa yini ɗaya da shan magani saɓanin ciwon daji.

Ta ce yawan shayarwa na kare mace kamuwa da Kansa kamar yanda akwai yiwuwar mace mai yawan haihuwa ta kamu da ciwon.

Ta yi kira ga mutane su cigaba da hakuri da gwamnatinsu su riƙa yin ƙorafin abin da ba su gamsu da shi ba a hanyar da ta da ce ba tare da zagi ko cin zarafi ba, za a saurara a ɗauki matakin da yakamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *