Spread the love

An Fara Gina mafi tsarin Wajen Wasa da Motsa Jiki a Jahar Sokoto Wanda Dan Kwallon Nageriya dan Asalin Jahar Sokoto Abdullahi Shehu Ke yi.

Aikin ya soma ne a wannan satin ana sa ran kammala shi nan ba da jimawa ba domin Sakkwatawa su amfana da shi ganin a jihar ana ƙishirwar irin wannan wurin.

Ɗan ƙwallon Nijeriya Abdullahi Shehu ya yi tunanin samar da irin wannan wurin na wasa da motsa jiki a jihar bayan takwaransa abokinsa Ahmed Musa ya samar da cibiyar wasan a jijar Kano.

Cibiyar motsa jikin za ta zama irinta ta farko a jihar wadda take ɗauke da kayan wasanni da Duniya ke yayi.

Managarciya ta so jin ta bakin Abdullahi Shehu domin samun bayani daga wurinsa filinsa ne ya saya ko gwamnatin jihar Sokoto ce ta cika alƙawalin da ta yi mishi na ba shi kyautar fili domin gina cibiyar.

A wata ziyarar da ɗan ƙwallon ya kai fadar gwamnatin jiha gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi alƙawalin kyautar fili da wani tallafin kuɗi ga ɗan ƙwallon, sama da shekara da wannan maganar ba a sake jin komai ba, sai ga wannan aikin an tayar da ya faranta ran matasan Sakkwato.

Cibiyar ana ginata bayan gidan man NNPC a tsakiyar birnin Sokoto, saura da mi akwai buƙatar uban tafiya ya tabbatar wannan cibiya za ta waƙilci Sokoto a fanin gudanarwa da ma’aikata.

Ɗan wasan a yau yana cikin lokacinsa kuma kusan shi ne na farko a jihar Sokoto da ya samu nasara sosai a harkar tamola, ana sa ran ya taimaki matasan jihar domin su ma su zama abin alfahari ga danginsu da jiha ɓaki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *