Spread the love

Gwamnatin jahar Sokoto ta rarraba magunguna da allurai ,da kayan binciken lafiya ga asibitocin kula da lafiyar dabbobi a yankunan jahar guda uku.

An smar da waɗannan kayayyakin ne tare da rabasu ta hannun maiakatar kula da lafiyar dabbobi da bunkasa noman kifi ta jahar, wanda aka yi a harabar asibitin dabbobi dake unguwar Aliyu jodi cikin garin Sokoto.

A wurin taron rarraba kayyakin ga yankunan, kwamishinan ma’aikatar Farfesa Abdulkadir Junaidu ya ce gwamnatin Sokoto ƙarƙashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal ta tanadi kayan, domin a ƙara samar da kayan aiki ga ofisoshin na yankunan jahar Sokoto masu kula da lafiyar dabbobi, hakan zai ba su damar gudanar da ayukkansu yadda ya kamata cikin nutsuwa da lumana.

Farfesa ya ce kula da lafiyar dabbobi wajibi ne saboda a magance rashin lafiyoyin da suke fama da su waɗanda suna iya sa mutane su kamu da su.

Ya ce wannan ne yasa Gwamna Tambuwal ya samar da wadannan magunguna da kayan aiki na zamani ga ofisoshin na kula da lafiyar dabbobi na yankuna.

Daga cikin Kayan da aka samar sun hada da kayan da ake amfani da su wurin dasa maniyin dabba cikin mahaifa domin samarda iri, naurar bincike ta tafi da gidanka,da naurar daukar hoto ta tafi da gidanka, da sauransu.

Haka ma an tanadi motocin daukar marasa lafiya na dabbobi, da motocin da likitocin zasu tafi wurin aiki lokacin da duk aka kirasu ,da babura domin sauƙaƙa zirga zirga na jama’ar jihar.

Gwamnatin Sokoto ƙarƙashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal ta yi ƙoƙari ainun a samar da waɗan nan kaya abin yabawa ne da fatar ɗaurewar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *