Spread the love

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC yankin Sokoto ta kama tare da bayar da belin Danladi Chindo, Daraktan kuɗi a ma’aikatat ƙananan hukumomin jihar Sokoto dawani Nasiru Umar duk a ma’aikar.
An kama su ne kan zargin sun yi sama da faɗi da wasu kuɗi da yawansu ya kai naira miliyan 6,703,000.
Hukumar ta ƙwato kuɗin, sun kama wanda ake zargin ne biyo bayan ƙorafi da wasu ma’aikata 63 dake ƙaramar hukumar Keɓɓe a Sokoto suna zargin an yi sama da faɗi da albashinsu tun daga watan Afirilu zuwa Satumba a 2019.
A binciken da hukumar ta yi ta gano an dakatar da biyan ma’aikatan ne su 63 kan dalilin wani zargi da bai da makama.
An dawo da kuɗin da zaran an kammala bincike za a kai wanda ake zargi kotu domin fuskantar shari’a.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a yankin Sokoto ya tabbadar kamen da belin ga Managarciya.

Abin jira a gani bayan kammala binciken wace kotu ce za a a hannunta ƙarar da yadda za ta kaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *