Spread the love

Jam’iyar PDP sun kalubalanci fadar shugaban kasa ta yi bayanin in da ake samun kudin da ake tafiyar da ofis din Uwar gidan shugaban kasa.

A bayanin da Sakataren yada labarai na kasa Kola Ologbodiyan ya fitar ya nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da aka rantsar da shi wa’adin mulki na farko ya yi alkawalin ba zai gudanar da ofis din Uwar gidan shugaban kasa ba.

Don haka akwai bukatar shugaba Buhari ya ba da misali kan yunkurinsa na rage kashe kudaden gwamnati ga umarnin da ya bayar wa Ministoci da sauran ma’aikatan gwamnati.

Duk da Jam’iyarsu ta fahimci fadar shugaban kasa ba ta fitar da kasafin kudin ofis din ba ga jama’a akwai zargin almundahana da kashe kudi a wurin.

PDP na bukatar Shugaban kasa ya sani duk abin da ya faru a wurin shi ne za a tambaya, ‘yan Nijeriya na bukatar karin bayani kan kudin da ake kashewa wurin.

PDP na nan tana bibiyar yanda ake bin umarnin shugaban kasa kan yanke kudin tafiyar da gwamnati da ya bukata ga jami’an gwamnati su aiwatar.

Haka kuma ta so Buhari ya cika alkawalin da ya dauka wurin rage facaka a fadar shugaban kasa ganin yanda mutanen kasar nan ke shan wahala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *