Spread the love

Sarkin Kannywood kuma jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu ya ce an karrama shi a Indiya, a zantawarsa da BBC.

Ya ce Wasu dalibai ‘yan Arewacin Najeriya da ke karatu a kasar Indiya da malamansu Indiyawa ne suka gayyaci shi bikin Ranar Al’adu kuma suka karrama shi a wajen taron.

Ɗaliban suna karatun fannoni daban-daban na likita zuwa hada magunguna da injiniyoyi da dai sauransu.

A Shirin taba kidi taba karatu ne ya faɗi haka ya ce baya ga wadannan ɗalibai, wasu makarantu a kasar sun ba shi lambobin yabo.

Ali Nuhu ya ce “akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba ni lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu.”

Tauraron ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha’awar al’adun Hausawa.

Wasu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe take.

Ya ji daɗin karramawar domin hakan ya nuna akwai masu kulawa da abin da yake yi da yabawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *