Bayan Tiriliyan 1.5 da aka batar a harkar wutar lantarki cikin shekara biyu, gwamanitn tarayyar Nijeriya ta ce ta fara shirin zuba wasu sabbin kudi dalar Amerika biliyan uku wanda kudin za su kama naira biliyan 915, bashi ne za a ciwo ga bankin duniya.

Ministan Kudi da kasafi da tsarin cigaban kasa Hajiya Zainab Ahmad ta bayyana haka a tattaunawarta da manema labarai a kan zamansu da bankin Duniya da sauran masu harkar kudade na kasa da kasa.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a watan Satumba ya ce gwamnatin tarayya ta zuba jarin kusan Tiriliyan 1.5 a haujin wutar lantarki cikin shekara biyu .

Osinbajo ya ce hakan a lokacin taronsu da kamfanin MESL dake Kanji a jihar Neja ya dauki nauyin gudanar da shi a watan da ya gabata.

Mataimakin shugaban kasar wanda ministan wutar lantarki Sale Mamman ya wakilta ya ce majalisar zartarwa ta kasa ta aminta da tallafi a kaso na uku a bangaren wanda za su kai 1.5 Tiriliyan cikin shekara biyu da suka wuce.

Sai ga shi kuma Ministan kudi a Washington DC ta ce muna tattaunawa da jami’an bankin duniya kan yanda za mu kashe kudin da za mu ranta na dala biliyan 3.5 da za mu sanya su a bangaren wutar lantarki.

Ministar ta ce bashin za a yi amfani da shi a samar da cigaban wuta da kuma karfafa raba ta.

Ta ce kuma bashin za a yi amfani da shi a magangace wasu matsaloli da bangaren wutar lantarki ke fama da shi a kasar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *