Hukumr yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi

Jami’an hukumar sun tafi gidan tdohon Gesmnan dake hanyar Nagogo a Kaduna da ƙarfe ɗaya na ranar yau Jumu’a in da suka tafi da shi.

Wata majiya ta kusa da iyalan shinkafin da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da an kama Shinkafin ga jaridar DAILY NIGERIAN.

Ya ce iyalan tsohon gwamnan ba su san in da aka tafi da shi ba zuwa yanzu.

A lokacin da aka tutuɓi mai magana da yawun hukumar ya ce yana buƙatar lokaci ya bincika kafin ya yi magana.

A ranar Alhamis EFCC sun gabatar da shedu uku kan shari’ar da suke yi da tsohon ministan kuɗi Bashir Yuguda da tsohon gwamnan Zamfara Mahmud Aliyu Shinkafi, Aminu Ahmed Nahuche da Ibrahim Mallaha a gaban mai shari’a Fatima Aminu a babbar kotun tarayya ta Gusau.

Hukumar tana shari’a da su kan zargin sun karɓi miliyan 450 ga hannun tsohuwar ministan kuɗi Diezani Alison-Madueke a zaɓen 2015.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *