Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da a fitar kudi da ywansu ya kai biliyan 10 a tallafi na musamman domin a gyara da kuma daukaka filin jirgin kasa da kasa dake Enugu wannan aikin ba a son a bata lokaci wajen aiwatar da shi.

Aminta da fitar da kudin ya zo ne bayan a yarin gwamnoni da shugabanin Kudu maso Gabas sun kai ziyarar ban girma ga shugaban kasa.

Filin jirgin an soma gyaransa a Agustan da ya gabata in an kammala aikin zai kara bunkasa cigaban yankin gaba daya da kasar baki daya.

Irin wannan ziyarar akwai bukatar gwamnonin Arewa maso Yamma su kai wa shugaban kasa ita domin samun damar gyaran hanyar Sokoto zuwa Kaduna da kammala aikin Kano zuwa Zariya da sauran hanyoyin gwamnatin tarayya a wannan yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *