Spread the love

Daga Safiya Usman.

Masu iya magana kan  yi wa mata kirari da cewa  ‘mata in ba ku ba gida….’, maza su yi mulki a waje su zo gida ku mulke su, abarku; ku sangarce a yi muku fada ku yi yaji, ku yi laifi aba ku hakuri,mata masu mayar da sarki bafade.

Ba shakka a lokacin baya mata suna cikin wasu nau’in al’umma da ake dubi domin koyi da nagartattun dabi’unsu, wanda  hakan ke sanya ana kallonsu a  matsayin masu taka rawa a tarbiyar ‘ya’ya musamman a cikin gidajensu, da ma wasu muhimman abubuwan da maza ba su cika sadaukar da kai wajen yin su ba. Masu iya Magana kan ce tarbiya daga gida take farawa.

A zamanin baya mata sun kasance masu kamun kai wanda ko abinci mace ba ta ci kan hanya, idan saurayi ya nemi yarinya aure kuma har ya ganta tana cin kwalama, tau da yamma  zai kai ziyara gidansu budurwar,  ya sayi nau’in abincin da ya ga tana ci ya kai wa iyayenta a matsayin kyauta, abin da ke nuna masu cewa tabbas ya ganta tana cin wani abu akan hanya. Daga nan uwayen za su kira ta su zaunar da ita su yi ta yi mata fada, ka ga wannan maganar abinci kenan fa.

To amma yanzu lokaci ya zo ba  kwalama ba har kayan shaye-shaye da ke sanya maye matanmu na wannan zamani sun tsundumma ciki  harkar  gadan- gadan,  abin da yanzu ya  zama ruwan dare gama gari, kuma wannan muguwar dabi’a ba ma ga manyan mata kawai ta tsaya ba, har ma ga ‘yan mata matasa wadan da shekarun su ya fara daga 15 zuwa 25, wadanda ya kamata  suna gidajensu na aure ko makaranta. Haka kuma wani abin ban mamaki da takaici shi ne mafi yawan ‘yan matan da ke tu’ammali  a  shaye-shayen  wannan lokaci Hausawa ne, kuma shaye-shayen bai tsaya kawai ga ‘yan mata masu gararanba a titunan ba, har da ma wadanda suka yi ban kwana da iyayensu da suka haife su(shiga yawon duniya), musibar ta kutsa har cikin matan da ke  gidajensu na aure. Abin da mafi yawan mutane ke tambaya shi ne, idan har matan da ba su da aure suna da damar fita waje su je duk in da suke so  su sayi irin wadannan kayan mayen, matan dake dakunan auren, su wace hanya su ke bi wajen samun kayan mayen da suke sha, shin wa ke saya musu, da kudin wa suke saya? Amsar wannan tambaya ita ce za mu fitar a cikin wanna rubutu.

Da yake masana sanin halayar dan adam sun bayyana cewa mafi yawan matan da suka rungumi wannan dabi’a sun sami kan su ne  cikin ta a dalilai daban-daban da suka hada da abokan zama a unguwa ko wajen biki ko  makaranta,  mafiyawan matan ba su la’akari da abokan da ya kamata su yi abokantaka da su.

Sanadiyar hakan ke sanya su fada wa hannun miyagun abokanai da za su ja hankalin su tare da saka su shiga wannan muguwar dabi’a da ba ta da  riba, ta hanyar taya musu kayan maye domin dandanawa da kuma nuna musu muhimmanci abin, wanda daga nan wasu sun fara kenan sai yadda hali ya yi, don za su rika samun shi kyauta  ba tare da sun  biya ko sisin kwabo ba, daga bisani idan ya zamo musu jiki za su rika amfani da kudin su wajen sayen kayan mayen  da ke sanya su rika fita hayyacinsu tare da canza tunananinsu da dukkkan abubuwan rayuwa, kuma ba za su iya tsinnna komai ba idan har ba su sha nau’in kwayoyin ko magungunan da suka saba sha ba.

Haka ma irin wadannan matan da ke shiga wannan sabga ba su cika damuwa da abin da za su ci ba fiye da su sayi magunguna domin biyan bukatunsu. Mafi yawan matasan matan da ke shiga wannan yanayi na shaye-shaye kan yi amfani da wasu dalilai dake sanya su amfani da kayan maye da suke ganin zasu kawar musu da shi kamar shiga yanayin nishadi ko kawar da bacin rai, ko son gamsar da namiji, ko kuma kwadayin sai an sha don ganin   wata abokiya ta sh. Wasu kuma suna amfani da kayan shaye shaye ne domin su yi rashin kunya ko tsageranci,  idan sun sha kunya da tsoro zai fita a zukatansu. Wasu mata kuma sun dogara ne  da yadda suke ganin mahaifansu na sha.Wasu kuma suna amfani da magungunan ne domin su taimaka musu wajen karatun jarabawa. Wasu kuma domin rashin daukar ciki(juna biyu). Irin wadannan dalilai suna da yawa wadan da ke sanya matanmu fadawa tsaka mai wuya, a rungumar kayan shaye-shyen da suka hada da Tabar wiwi, hodar iblis, nau’in maganin mura, da kwayar roci da ta doki ko sunsunar bayan gida.

Abin ban haushi mafi yawan matan da suka shiga wannan lalura ba su cika damuwa da tunanin aure ko karatu ba, saboda  auren baya gaban su.Wasu kuma da yawan su ba su san illar da kwayoyin ke yi musu ba, duk da yake akwai masu ilmi da ke shiga wannan sana’a  sun  san lahanin da magungunan ke yi musu a rayuwa, amma sun ki bari don harkar nada wuyar bari, musamman wadan da suka dauka rayuwa ce ba za su daina shan  ba.

 Daga cikin illolin da kan shafi mata masu shaye shaye dama dangin su da al’ummar da matan ke ciki na farko kyama a cikin al’umma da kuma rashin tsayar da ibada don gushewar hankali, daukar curutoci, gushewar hankali gaba daya, shiga mugun yanayi, tsageranci da rashin tausayi, a aukuwar fyade ko madigo da  shiga hadarin yin sata, mutuwar aure da shiga harkar karuwanci da sauransu.

Idan muka kalli yadda yawaitar mutuwar aure ta yi tasiri musamman a kan zargin shaye-shaye ga matan aure, saboda mafi yawan matam auren da ke shaye-shaye mazajensu ba su da masaniya kuma da zaran sun gano matan suna shaye-shayen za su raba hanya da su. kuma idan har auren ya watse sai kaga matar ta cigaba da shiga halin kaka nika yi wata kila ma ya barta da yara kankana wadan da ba shakka idan har suna hannun ta ba yadda za’a yi tarbiyar su ta kasance mai inganci a hannunta. Wannan dabi’a da wasu matasan matan mu suka tsunduma na shaye-shayen  kwayoyi wata gobara ce da ya kamata a ce al’umma su tashi tsaye wajen ganin cewa an shawo kan al’amarin, saboda ko wace cuta tana da magani, kuma kowa ce matsala tana da mafita, don haka wannan mummunan hali da matanmu suka shiga ya zama wajibi kowane bangare na al’umma su yi tunanin hanyoyin da za’abi don  kawar da wannan matsalar baki daya, saboda illar shaye-shaye bai tsaya kawai ga masu sha ba, har ma ga al’ummar da wadannan yaran suke cikinsu. saboda haka wannan gudumawar ta ta’allaka ne ga kowa da kowa, kama da iyaye wadan da su ne sahun farko da ya kamata su dauki matakin sanya ido wajen tarbiyar ‘ya’yan su tun daga matakin farko. Dole su lura da yadda ‘ya’yan su mata ke hulda da abokanin su da inda suke tafiya hira a wasu gidajen matan aure, don da  yawa zaka ga a unguwa,’yan mata sukan sami wajen zama ne a wani gidan matar aure da sunan taya ta hira, sai wurin ya  koma  majalisar zawarawan unguwa, suna zama matattarar wadannan mata masu irin wannan muguwar dabi’a, wanda mafiyawan ‘yan matan sukan koya ne a wajen su.Ya kamata a duk lokacin da iyaye suka ga yarinya da wani nau’in magani na kwaya ko na ruwa,ya zama wajibi su bincike su domin sanin mine ne ya sanya amfani da shi? Haka ma ya kamata iyaye su rika kai ziyarar ba za ta musamman a dakunan kwanan ‘ya’yansu mata da kuma bincikar jikkunansu musamman wadan da suke ratayawa alokacin da za su fita.  Ya kamata a duk lokacin da iyaye suka ga yarinya ta faye yin bacci ba gaira ba dalili, ya zama wajibi a wajen su su gano mine ne dalili, domin wannan sabga ta bacci a koda yaushe tana daya daga cikin alamomin da ke nuna yarinya ta shiga harkar shaye-shaye gadan gadan, ka da a rika sanya ‘ya’ya mata aikin karfi da yafi karfin su domin kuwa yin hakan zai iya saka su shiga harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi saboda, idan ba su sha ba, ba za su iya yin wannan aiki da aka saka su ba.

 Hukumomi ya kamata  su yi kokari wajen ganin cewa sun samar da ayukan yi  ga matasa mata wadan da suka kamala karatun su na sakandare da ma na gaba da sakandare,  domin samun aikin da zai hana musu amfani da wani lokaci da za su hadu da miyagun matan da za su saka su hanyar shaye-shaye, bayan  wannan  hukumomi su fito da wata doka ta hana sayar da miyagun magunguna a shagunan sayar da magani a birni da karkara da ma wadan da ke sayar da magunguna a cikin  kwandon roba, a  rika fitowa da shiraruwan nan da ake kira auren gwabnati,wanda gwabanati ke daukar nauyin aurar da mata da maza a cikin aljihunta, domin hakan yakan rage yawaitar mata dake gararanba a cikin unguwanni da  kan tituna. Mutanen  unguwa su rika fitowa da tsarin aurar da diyansu ga diyan makwabci, idan har suna son junansu kuma akwai halayen kirki a wurinsu, wannan zai taimaka wajen ganin yaran ba su yi nisa da mahaifan su ba har a yi tunanin za su iya shiga wannan sabga. Ya zama wajibi makwabta su dawo da tsarin nan da ake kallo ya zama tsohon yayi wanda kuma ke kawo fada tsakanin juna na tsawatar da ‘ya’yan makwabci idan aka ganshi yana aikata abin da ba daidai ba. kungiyoyin malaman addinin musulunci,  boko da kafafen yada labarai, masu shirya finafinnai mawaka, marubuta, da fadakar  da masu sha da ma wadan da ke da sha’awar fara shan, su san illolin wannan bahaguwar sana’a maras riba, da ta kunno kai a cikin matasan matan mu da ma manyan mata domin yiwa tubkar  hanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *