Spread the love

Maryam Sanda wadda ake zargi da kashe mijinta Bilyaminu Bello ta ba da nata bayani a gaban kotu abin da ta sani kan yadda mijinta ya rasa ransa.

Ana shari’a da ita a gaban babbar kotu dake Abuja mai mazauni a unguwar Maitama da zargin ta kashe mijinta wanda yake dan uwa ne ga tsohon ciyaman na jam’iyar PDP Alhaji Bello Haliru Muhammad a shekarar 2017.

A lokacin da abin ya faru ‘yan sanda sun tsare ta tare da dan uwanta Aliyu Sanda da da mahaifiyarta Maimuna Aliyu da ‘yar aikin gidanta Sadiya Aminu kan zargin da aka yi masu na son boye gaskiyar lamari, in da suka taimaki mailaifin aka wanke duk wurin da jinin margayi ya diga a lokacin aikata mummunan laifin.

Kotu ta sallame su ga zargin da ‘yan sanda suka yi masu.

An dawo sauraren karar laifin da ake zargin Maryam da aikatawa in da ta bayar da nata bayani tana cikin zubar da hawaye da alhinin yanda aurenta bayan shekara biyu ya kai karshe ta ce ita ba ta kashe mijinta ba.

Ta fadawa kotu a 18 ga watan Nuwamba na 2017, ta dauki wayar mijinta margayi ta kira wata namba, anan ne ta ga hotunan tsiraici na wata budurwa sai ta sauka kasa domin ita tana gidan sama ne domin su yi magana da margayin.

Ta ciga da fadin a tattaunawar da suke yi ne sai gardama ta kaure tsakaninsu, har ta nemi mijin ya sake ta, a wurin dai har da shaƙe wuyanta ya yi sai da ta yi ƙara.

Gardamar ta ci gaba har zuwa 11 na dare, ta tafi ta dauko cajarta dakin kwana, anan ne ya ɗungujeta ta faɗi kasa, a hakan ne ba da gangan ba ta fashe kwalbar Shisha ruwan dake ciki suka zube ga daben dakin.

Tace margayi ya danneta ƙasa, kuma ta faɗa masa ya ɗaga mata ta je ta ɗauko ɗiyarsu da ta ji kukanta da yaƙi ta kucce, a ƙoƙarinsa na riƙe ta ya faɗi, daga nan ta ga margayin ya riƙe ƙirjinsa da fasassar kwalbar bayan ta cire mashi ta ga ƙirjinsa ya tsage.

Ta ce ta sheƙa da gudu ta kira Ayuba don ya taimaka mata suka kai mijinta ƙaramar adibiti a Abuja, a in da aka tabbatar Bilyaminu ya rasu. Aka sake kai shi babbar asibiti Maitama a can ma aka tabbatar da rasuwarsa.

Daga asibiti ne taje ofis ɗin ‘yan sanda a Maitama ta rubuta bayaninta.

Ta je shedannun da aka gabatar wai ita ta kashe mijinta ba gaskiya ba ne

“Ban yi yunƙirin kashe mijina ba. Mun dai yi gardama. Ban so mijina ya rasu ba” Maryam Sanda ta faɗawa kotu.

Alƙalin kotu Yusuf Halilu ya ɗage sauraren ƙarar zuwa Nuwamba 25 don tabbatar da bayanai na ƙarshe, daga haka sai yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *