Spread the love

An yikira ga Al’ummar kauyen Tafkin kada dake cikin karamar Hukumar mulki ta jega dake jihar Kebbi da su cigaba da gudanar da lamurran su na yau da kullum tare da kai rahoton bakuwar huskar da basu amince da ita ba ga Hukumomi don daukar mataki.

Mataimakin Gwamnan jihar kebbi Alhaji Sama’ila Yombe Dabai ne yayi wannan kiran a lokacin da yake cigaba da ziyar tabbatar da karin samun zaman lafiya a ynkin.

Alhaji Samaila Yombe Dabai har ila yau dai, yakara jaddada Kudurin Gwamnatin jihar nan a karkashin jagoran cin Gwamnan jiha Sanata Abubakar Atiku Bagudu na bazata yi kasa a gwaiwa ba na tabbatar da cigaba da kara ingata sha’anin tsaro a ciki da wajan jahar nan ta kebbi, inda yace sai da tsaro ne ake samun cigaban kasa .

Mataimakin Gwamnan ya ya amfani da damar inda ya kara jinjina wa ga jami’an tsaron akan irin namijin kokarin su tare da cewar za su yi aiki tukuru domin samun nasarar kauda Miyagun a yanki.

Alhaji Samaila Yombe Dabai yace yazamo wajibi na daukar dukkanin matakan da suka dace akan iyakokin jihar nan musamman iyakokin zamfara sokoto da Nija.

Tun farko mataimakin Gwamnan Alhaji Sama’ila Yombe Dabai yagana da tawagar jami’an soji da yan sanda da sauransu inda yanuna jindadinsa akan kulawar su .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *