Spread the love

Kwamishinan Kuɗi Na Jihar Bauchi Alhaji Nura Manu Soro, Yayi Murabus Kan Mukaminsa Na Kwamishinan Kudi, In da Ya Bayyana Hakan A Shafinsa Na Sada Zumunta na Facebook, A Safiyar Laraba, Inda Yace Zai Bayyana a Gaban ‘Yan Jaridu Domin Jin Ta Bakinsa Idan Allah Ya Yarda Zuwa Wani Lokaci.

Saidai A Fannin Gwamnatin Jihar Bauchi Kuma Bayan Alhaji Nura Manu Soro, Ya Bayyana Murabus ɗinsa Sun Fitar da Sanarwa ta hannun Kwamishinan Yaɗa Labarai cewa, an Samu sauye-sauye wuraren aiyuka ga Kwamishinonin Jihar Bauchi Inda Aka Maida Kwamishinan Kudin Zuwa Mukamin Kwamishinan Wasanni Da Matasa.

Alhaji Nura Manu Soro dai na Daga Cikin wayanda suka taka Rawar Gani a Lokacin Gwamnan Jahar Bauchi Bala Muhammad na neman kujerar gwamna.

Bayan Samun nasarar Gwaman Bauchi Bala Muhammad Mutane da dama sun ɗauka a Bawa Nura Matsayin Sakataren Gwamnati duba ga Irin Gudumuwa da Kwarewar aikinsa.

Da aka ba shi kwamishinan kuɗi ya ce bayan wannan kujera da ma’aikatar babu wata, ana ganin dalilinsa na yin murabus domin bai gamsu da in da aka kai shi ba duk da rawar da ya taka a lokacin neman kijerar gwamna.

Wasu na ganin in dai don maganar aiki ne bai kamata ya ajiye aiki ba. Komi ne dai za a ji a lokacin da zai yi magana da manema labarai.

Daga, Jamilu Sani Rarah Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *