Spread the love

Jami’an Kwastam sun kashe wani mutum mai suna Tasi’u Muhammad a garin Babura dake jihar Jigawa, saboda zargin da hukumar fasa kwabrin take yi masa na ya zama mai leken asiri da bayar da bayani ga masu yin sumogalin din shinkafa a hanyar Babban Mutum kan iyakar Nijeriya da Nijar(Infoma).

Jaridar daily trust ta samu bayanin margayin yana cikin jerin sunayen da hukumar ke nema ruwa jallo, an sanshi da aikata laifi a kan iyakar a Babban mutum ta Katsina da Babura ta jihar Jigawa.

Margayi yana cikin wadan da ake zargi sun hanawa ma’aikata aiki yanda yakamata a saman hanyar bayar rufe boda da aka yi.

An zarge shi bayan zamansa Infoma in jami’an kwastam na sintiri har da nunawa masu sumogalin din hanyoyin da za su bi kar a kama su.

Jami’an sun kashe mutumin ne a Anguwan Gawo garin bai da wani nisa da Babura.

Jami’in Kwastam Isa Danbaba ya ki daga wayar wakilin daily trust, har zuwa hada rahotonsa, amma kwamishinan ‘yan sandan Jigawa Bala zama ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *