Bayan kwana 40 da rantsar da kwamishina ya ajiye muƙaminsa a Bauchi

Tsohon Kwamishinan kudi da aka mayar ma’aikatar matasa da wasanni na jihar Bauchi Nura Manu Soro ya yi murabus daga kujerar shi bayan da gwamna ya yi wa kwamishinoninsa sauyin ma’aikatu, Nura ya yi murabus kwanaki ba su wuce 40 ba da rantsar dasu a matsayin Kwamishina.

Ko miye dalilin Nura na ajiye aiki kwanaki kaɗan da soma aikinsa.

Gwamnan Bauchi bai yi magana kan ajiye muƙamin ba na ko ya karɓa ajiyewar ko bai karɓa ba.

Wannan kwamishinan shi ne na farko da ya yi haka shima bai sanar da dalilin ajiye muƙamin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *