Rahotanni wanda Managarciya ba ta tabbatar ba sun bayyana cewar, Kotun majistiret mai lamba 15 karkashin mai sharia Muntari Garba Dandago ta aike da wata mata mai suna Sadiya Haruna gidan gyaran hali.

Tun farko ‘yan sanda ne suka gurfanar da ita bisa zargin ɓata suna, laifin da ya saɓa sashi na 391 na kundin hukunta masu laifin Penal code.

A yayin zaman kotun mai shari’a Muntari Garba ya karanta tuhumar ya bayyana cewar wani mashiryin shirin Hausa mai suna Isa A. Isa shi ne yayi ƙorafin a kan Sadiyar ta ɓata masa suna.

Akwai wani fefan murya da Sadiyar ta nuna ta yi kalaman ne domin huce haushinta ga abin da saurayinta Isa ya yi mata na shareta kan cutar da shi ne sillarta, ya kuma koma kan wata yarinya har yana saka hotonta da kalaman soyayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *