Spread the love

Ɗan takarar Gwamnan jihar Sakkwato na Jam’iyyar APC Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto da Jam’iyyar ta APC a yau Laraba sun garzaya kotun ɗaukaka kara, kan rashin aminta da hukuncin kotun sauraren zaɓen Gwamna da ta yi zamanta a Sakkwato ta yanke hukunci a Abuja domin bi masa kadinsa, kamar yadda ɗaya daga cikin mambobin Lauyoyin Jam’iyyar APC Barista Bashir Mu’azu Joɗi ya sanarwa manema labarai.

Makwanni biyu da suka gabata kotun sauraren ƙarar zaben Gwamna a wani zama da ta yi a Abuja ta ce bata gamsu da hujjojin mai ƙara ba ya kasa gamsar da kotu maganar a ringizon ƙuri’u da saɓawa dokokin zaɓe kan haka Aminu Tambuwal halastaccen Gwamna ne.

Kan wannan halin Ahmad Aliyu da APC sun ƙalubalanci hukuncin na kotun zaɓen Gwamna in da suke neman a sake duban hukuncin da idon basira.

Kotun dake zamanta a jihar Sakkwato kan titin Kaduna ta karɓi ƙarar abin jira a gani yanda za ta kaya a kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *