Spread the love

Cutar shawara waton yellow fever annobar ciwon ta ɓulla a jihar Bauchi ta kashe mutum 22 a halin da ake ciki.

Hukumar kula da lafiya matakin farko ta tabbatar da rasa rayukkan mutum shidda bayan 17 sun rasu a can baya.

Sakataren hukumar Dakta Rilwan Muhammad ya ce sun samu bayanin cutar a wurare daban daban aƙalla 143 daga cikinsu an tabbatar da 24, mutum 22 suka rasu.

Muhammad ya ce 10 daga cikin 22 mutanen yankari ne amma dukan masu cutar a ƙaramar hukumar Alkaleri suke.

A rigakafin cutar da aka yi an sami 79 na waɗanda suka amfana da maganin cutar vector mai ɗauke da sinadarin cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *