Spread the love

Babu Yunwa A Nijeriya Domin Da Naira Talatin Sai Ka Ci Abinci Ka Koshi A Kano, in ji Ministan Noma, Sabo Nanono

Ministan noma, Sabo Nanono a jiya Litinin ya bayyana cewa Nijeriya tana samar da iasasun abinci da za ta iya ciyar da al’ummar ta har ma ta aike da saura zuwa kasashen dake makwabtaka da ita.

Jaridar ‘The Punch’ ta ruwaito cewa Nanono ya ce koken da ‘yan Nijeriya ke yi na yunwa a kasar abin dariya ne, inda ya ce babu yunwa a Nijeriya.

Yayin jawabin da ministan ya yi a wurin taron manema labarai don bikin ranar Abinci na Duniya ta 2019 a Abuja, ya ce, “Ina tunanin muna noma wadataccen abinci da zai ciyar da mu. Ina ganin babu yunwa a Nijeriya. Idan na ji mutane suna maganar yunwa a wannan gwamnatin, na kan yi dariya ne kawai.”

A cewar Nanono, abinci yana da araha sosai a Nijeriya idan aka kwatanta da sauran kasashe.

Ya ce, “A kasar nan, babu tsadar siyan abinci da mutane za su ci. Misali jiha kamar Kano za ka iya sayen abincin naira talatin ka ci ka koshi”

Ya ce gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasar ne domin saka dokokin da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya keyi inda suka mayar da Najeriya bolar zubar da shinkafa da ta lalace da sauran kayayyaki.

Nanono ya ce, “Wannan shine ainihin dalilin da yasa aka rufe iyakokin kasar kuma ina ganin Najeriya tayi kokarin fahimtar da kasashen amma ba su yarda ba.

“Muddin har kasashen ba za su mutunta Najeriya suyi biyaya ga dokokin shige da fice ba kan shigo da abinci, iyakokin Najeriya za su cigaba da kasance a rufe.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *