Spread the love

Daga Nasiru Zango.

Mutanen Kano dana Arewa suna buƙatar a yi masu adalci kan yaran da aka sace waɗan da aka gani da waɗan da ba a gani ba.

Ya zama wajibi mu bibiyi maganar satar Yara daga Kano zuwa Anambra wanda ya zama wani abin takaici dake nuna tsantsar rashin gatan talakan Arewacin Nigeria.

Domin Sama da shekaru 3, iyayen yaran ke kukan cewar Ana satar musu ‘ya’ ya Amma a gaskiya a Wancan lokacin basu Sami goyon baya sosai ba, sai dai Dan abin da ba’a rasa ba, a Wancan lokacin mun yi ta bin maganar tare da iyayen yaran.

Bazan ja doguwar magana ba, domin gaskiya ta fara fitowa, Amma fa akwai sauran Yara da ake nema wadanda har yanzu ba a Gano su ba.

Tun Wancan lokaci iyayen yaran sun yi kungiya, suka kuma fitar da lissafin Yara 47 ne suka bace, idan Baku manta ba, har Kalanda suka fitar Mai kunshe da hotunan wasu daga cikin yaran, Dan haka ne ma yanzu za a fara fafutukar, neman ganin an fito da sauran yaran, da kuma tabbatar da adalci akan masu hannu cikin wannan balahira. Allah ya sa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *