Spread the love

Kungiyar kwadago ta Nijeriya ta ce ba gudu ba ja da baya kan shirinta na shiga yajin aikin gama gari bayan ranar Laraba.

Ranar 16 ga Okotoba ne ranar da wa’adin da kungiyar ta baiwa gwamnatin tarayya ta aminta da fara biyan mafi karancin albashin dubu 30 ga ma’aikata ko ta shiga yajin aikin gama gari.

Bayan zaman tattauna wa da kungiyar gwamnati ta sake saka lokacin zama abin da ake kallon wasu daga cikin gwamnati na hana tabbatar lamarin.

Kungiyar ta ce duk wani taron tattaunawa da ministan zai kira ba tare da kwamitin yarjejeniya ba, ba wani hukunci da za a yanke a wurin da za su yi amfani da shi

Mambobinsu sun tsaya cik da shirinsu nako ta kwana da zaran ba a shirya ba da kungiyar shugabanninsu na jihohi za su umarce su da tsunduma cikin yajin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *