Spread the love

Uwargidan shugaban ƙasa Hajiya Aisha Buhari ta dawo Nijeriya bayan kwashe wata uku a ƙasar Saudiya da Ingila.

Aisha ta dawo da Asubar yau Lahadi ta samu tarba wajen hadimanta abin da ta yi farinciki da shi.

Bayan saukarta a jirgi mallakar ƙasar Ingila ta zanta da manema labarai ta nuna farincikinta da irin goyon bayan da suke samu ita da mijinta ga mutanen Nijeriya ta yi godiya kan haka.

Ta bayyana dalilinta na ɗaukar lokaci a waje domin ta zauna da ‘ya’yanta kuma a duba lafiyarta.

Ta ƙaryata masu yaɗa jitajitar ta yi yaji da masu cewa Buhari zai ƙara aure.

Ta yi shaguɓe kan minista Sadiya da taƙi ƙaryata zancen har sai bayan ranar da masu yaɗa ƙaryar suka aiyana za a yi auren.

Ma’ana kenan minista ba ta zaci ba za a yi auren ba. In haka ne ko ƙila akwai maganar ko mine ne dai in lokaci yayi za a ji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *