Spread the love

Dsga Bashir Sharfadi.

Wata sabuwar dambarwa ta barke a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood tsakanin jarumi kuma mashiryin finafinan Hausa wato Isa I. Isa da kuma jaruma Sadiya Haruna wadda ta yi kaurin suna a shafukan soshiyal midiya.

Dambarwar dai ta faro asali ne biyo bayan zarge-zargen da Sadiyar ta jefa kan jarumin, tun kafin ta kama sunansa, wanda a karshe kuma ta kama sunansa.

Daga cikin zarge-zargen dai akwai cewa sunyi auren mutu’a (auren sha’awa) a cewar ta cikin wani bidiyo da ta saki.

Jarumar ta kalubalanci jarumin da ya fito ya kare kansa game da kalubalantarsa da tayi.

Sai dai shi ma jarumin tuni ya wallafa wani bidiyo a shafinsa inda yake bayyanawa duniya cewa ya aikata wasu abu na ba dai-dai ba da yake neman gafarar al’umma, daga bisani ya goge bidiyon daga shafinsa, amma ina tuni bidiyon ya karade dandalin YouTube.

A kwanakin baya dai jarumin yayi wani bidiyo da yake bayanin cewa ana ta tambayarsa shin meye alakarsa da Sadiya Haruna?, inda ya bayyanawa duniya cewa matarsa ce.
Sa’o’I uku da suka wuce Sadiyan ta wallafa a shafinta na Instagram cewa Isa ya kawo mata ‘yansanda har gida kamar yadda kuke gani a kasa.

A kwanakin baya ma dai an tafka makamanciyar irin wannan dambarwa a tsakanin Sadiyan da kuma wasu jaruman finafinan, inda ta zargi wasu daga ciki da aikata badala.

Saidai jaruma Teema Makamashi ta kalubalance ta inda ta bayyana cewa jami’an tsaro sun samu nasarar cafke Sadiyan a ofishin jarumin Isa A. Isah.

Ita ma dai daya daga cikin manyan jaruman dake taka leda a soshiyal midiya Muneerat Abdussalam ta bayyana mamakinta da faruwar wannan rikici, inda ta bayyana Sadiya da Isa matsayin wasu masoyan biyu da suka taba kai mata ziyara.

Allah ya kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *