Spread the love

A Yaune Al’umma Musulmai Mata na Kasar Ghana Suka Fito Zanga Zanga dan Nuna Rashin amincewar da dokar hana Sanya Hijabi a ƙasar,
Zanga Zanga tasamu Halarta dubban Jama’a Waɗanda Ba Musulmai Ba
Yanda Mahalarta Zanga Zanga Sukayi Yawo da Kwalaye dake ɗauke da rubutu daban daban wanda Ke nuni da a kundin tsarin Mulki ƙasar ta 1992 ta Ba da dama ga duk Dan ƙasa Yayi addinin da yake so, batare da tsangwama ba.

Don haka matan sun fito domin a janye dokar don ta saɓawa tsarin ƙasa.

Matan sun nuna ba za su bar tsarin addininsu ba don haka abar su su yi addininsu yanda aka koya masu.

Masu zanga-zangar sun ɗauki lokaci suna yi kuma sun gama lafiya ba tare da samun tsangwamar gwamnati ba.

Matan suna fatan a barsu su ci gaba da sanya hijabi a ƙasar ba tare da kowane irin cikas ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *