Spread the love

Babban wanda ake zargi da kashe shugabar Sikandaren ‘ya’yan sojoji dake Jaji, Kwamanda Oluyemisi Ogundana ya shiga hannu.

Wanda ake tuhumar Benard Simon ya bayyana yadda ya kashe babbar sojar da ta kai matakin Nabal(Naval Officer).

Simon wanda yana cikin mutane 50 da hukumar ‘yan sandan Kaduna ta gabatar wa jama’a kan zargin laifuka daban-daban.

Kwamishinan ‘yan sanda Ali Aji Janga ya ce matashin shi ne ya kashe Kwamadar shi kadai bayan ya yi mata fyade.

Simon ya ce a zantawarsa da manema labarai a wurin ‘yan sanda shi kadai ne ya kashe sojar amma bai yi mata fyade ba.

Ya ce ya sulala ya shiga cikin gidanta dake jajin ya buga mata rodu saman kai abin da yayi sanadin barinta duniya.

Ya ce “Ni kadai na kashe ta na shiga gidanta da marece na buga mata karfen rodu ga kai. Na kasheta ne saboda tana walakanta mu cikin makaranta. Ni malami ne a makarantar tana walakanta dukkan ma’aikacin da ke karkashinta, na kashe ta saboda dukkan wadanda take walakantawa su samu sakewa daga walakancinta.”a cewarsa.

Ya ce akwai abubuwan da suke yi na samun kudi ta hana su shi karan kansa ma ta tare masa hanyar fiye da dubu 100, don haka ya kashe ta da kansa don ma’aikatan su huta da ita.

Haka kuma ya aminta ya aikata abin da ya yi dana-sani kansa na sassare namanta ya zuba cikin jikka ya jefa ta cikin wata matattar rijiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *