Spread the love

Kusan sati daya kenan bayan an yi garkuwa da dalibai mata su shidda da malamansu biyu na Kwalejin Engravers dake jihar Kaduna, ‘yan sanda sun ce sun san wurin da aka boye mutanen amma gudun hadarin da mutanen da aka tsare za su shiga ne ya sa ba su yi amfani da karfi ba don su kubutar da su.

‘Yan sandan sun ce sun shiga yarjejeniya da wadan da suka yi garkuwa da mutanen.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna Ali Janga ya bayyana hakan da yake yin bayani kan maganar.

Ya ce suna kan yarjejeniya da masu garkuwa da mutanen su saki dalibban da malamansu, ‘Mun san in da suke amma mun ki zuwa gudun kar mu sanya rayuwar mutanen cikin hadari’ a cewarsa.

Ya ce mafi yawan masu aikata laifin suna yi ne a lokacin da hankalinsu ya gushe kisa ba wani abu ba ne a wurinsu, don haka suka tsaya suna yarjejeniya da su ba da jimawa ba za a saki mutanen.

‘Muna baiwa mutanen kaduna nan ba da dadewa ba za mu kama masu garkuwa da mutanen’

Daga cikin matan da aka tafi da su akwai mataimakiyar shugaban makaranta a bangaren karatu da jagorar gida ta kwalejin dake Kakau Daji a karamar hukumar Chikun ta Kaduna da safiyar Alhamis ta satin da ta gabata.

Masu Garkuwan a Litinin da ta wuce sun nemi a ba su fansar miliyan 10 ga kowane mutum, bayan sun jingine maganar miliyan 50 ga mutum takwas gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *