Spread the love

‘Yan sanda a jihar Neja sun kama wani dan shekara 40 mai suna Sama’ila Shu’aibu kan zargin ya hukunta dansa mai shekara 6 Habibu abin da ya yi sanadin barinsa duniya.

Alhaji Adamu Usman kwamishinan ‘yan sanda jihar ya tabbatar da kamen a birnin Mina.

Usman ya ce wani dan kasa ne nagari dake unguwar Tunga Maje cikin karamar hukumar Suleja a jihar a inda wanda ake zargi yake da gida, shi ne ya kawo maganar wurin ‘yan sanda

Kwamishinan ya zargi Shu’aibu yana koyar da dansa margayi abubuwan da ba su dace ba a gida da ya kasa yin yanda yake so ne sai ya buge shi abin da yakai ga rasa ransa kenan..

Ya ce wanda ake zargi ya yarda da laifinsa ya ce bai dauki hukuncin da ya yi wa dansa zai kai shi ga rasa ransa ba.

Ya ce sun soma bincike in sun kammala za su kai wanda ake zargi kotu.

Ya yi kira ga uwaye su daina hukunta yaransu yanda suka ga dama masu yin haka in suka kama su za su hukunta su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *