Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce arzikin Nijeriya ya takaitu ga hannuwan wasu tsirarrun mutane dake zaune a jihohi 4 ko 5 da Abuja.

Ya ce Kusan mutum miliyan 150 a jihahi 31 suna cikin talauci.

Haka kuma Buhari ya fahimci cewa kammala zaben 2019 da aka yi lami lafiya kokari ne na wadan da suka samu nasara, abin da yafi kawai a mayar da hankali ga sanya farinciki ga mutanen kasa a inganta harkar tsaro da kawar da cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati, da kara inganta tattalin arziki.

Buhari a jawabinsa ga mahalarta taron tattalin arzikin Nijeriya karo na 25 a Abuja.

Ya ce wasu daga cikin mutanen da ake fadi suna cikin dakin taron, shi yafi mayar da hankalinsa ga farfado da tattalinarzikin ko da masu arzikin ba su bukatan haka.

Ya ce a lokacin yakin neman zabe kusan dukkan ‘yan takara sun nuna kudirinsu na son farfado da tattalin arziki a kasar nan.

Ya ce Jam’iyarsu ta APC ta fito da tsarin abin da za ta fi mayar da hankali gare su irin kara karfafa harkar tsaro da kawar da rashawa da samar da aikin yi da kara karfafa walwalar jama’a ga masu tsananin talauci da mabukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *