Spread the love

Mutum talatin da takwas sun nutse a cikin gulbin Kirfi a karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauchi, jirgin ruwa kwalekwale da suke ciki ne ya yi hatsari ya jirki ce da su, a bayana da manema labarai suka samu.

Shugaban karamar hukumar Kirfi Alhaji Bappa Danmalikin Bara a zantawarsa da manema labarai ya ce “Ina matukar jajantawa mutanen Kirfi, da jihar Bauchi da Nijeriya gaba daya kan rasa ‘yan uwanmu da muka yi kan hanyar su ta zuwa gona.

“Sun shiga jirgin ruwa na kwale-kwale su 40 abin tashin hankali mutum 38 sun nutse, mutum biyu ne kawai suka tsira. Mun ga gawar mutum biyu kan hanyar Badara, duk kokarin da muka yi na gano wasu har yanzu dai ba wani labari. Muna zaton dukansu sun mutu. Don haka muke rokon Allah ya gafarta musu laifukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *