Spread the love

Biyo bayan wani faifan bidiyo na minti 13 kan neman yin lalata da mace kafin a ba ta maki da kafar yaɗa labaru ta BBC ta fitar ya sanya hukumar jami’ar Lagas ta dakatar da Dakta Boniface Igbeneghu malami a sashen Turanci.

Dakta an same shi cikin hoton yana son aikata masha’a.

Jami’ar ta kira taron gaggawa kan lamarin ta kai matsayar dakatar da shi har baba ta gani.

BBC Afirika Eye bayan sun tattauna da ɗalibbai kan cin zarafi da nemansu da ake yi domin aba su maki, sai suka yanke shawarar tura’yar jarida ɗaya amatsayin ɗaliba domin tabbatar gaskiya.

Boniface wanda yake fasto ne a cochin Gospel a Lagas ganin farko da ya fara yi wa ‘yar jsridar mai shekarru 17 a lokacin da take neman gurbin karatu ya yaba shigarta.

Ya kuma bayyana mata akwai wurin da ma’aikata ke hutawa da kuma in da malamai ke tafiya da mata domin biyan buƙatunsu.

Haɗuwar ƙarshe da ya yi da ‘yar jaridar a ɗakin hutawarsu ya so ya yi lalata da ita.

Wannan bidiyon da aka saki ya fito ƙarara da baiyana irin yanda sheɗanun malamai a jami’oi da manyan makarantu ke sanya ɗalibai mata a gaba sai sun ci zarafinsu da walaƙanta mutuncinsu.

Akwai buƙatar uwaye su tashi tsaye wajen ganin sun kare mutuncin ɗiyansu mata, ka da hakan ya sa su karaya ga tura su makaranta a dai kula sosai.

dakatar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *