Spread the love

Kungiyar Malaman jami’a (ASSU) ta rabu gida biyu in da aka kafa wata sabuwa da aka kira haduwar malaman Jami’a(congress of University Academics).

Mabbobin kungiyar malaman jami’a ne suka kirkiri wannan sabuwar don samar da karsashin kungiyanci da daurewar zaman lafiya da wanzuwar kungiyoyi a Nijeriya.

Sabon Kodinata na kasa na kunginyar Niyi Ismaheel ya sanar da wannan a farkon zaman masu ruwa da tsaki da aka yi a Obafemi Awolowo dake Ile-Ife, kwanannan.

Da yake magana da manema labarai ya ce an fitar da sabuwar kungiyar ne domin canja salon samar da walwalar mambobi da magance matsalar lalata lokacin dalibai a wurin yajin aiki.

Kungiyar ta fara ne a OAU tana da mambobi a Jami’ar Ambrose Alli Ekpoma da jami’ar gwamnatin tarayya ta Ekiti da ta Lokoja jihar Kwara da jami’ar Molete.

A kalaman ministan Kwadago da aikin yi Chris Ngige ya ce kungiyar ba a yi mata rijista ba.

Ya ce ba su yi mata rijista ba har yanzu, neman izinin rijista yana kan teburinsa, bai yi aiki kansa ba, zai duba takardun bayanan nemansu, ya kafa kwamitin da zai yi aiki kan bukatarsu ta rijista.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *