Spread the love

Kungiyar Malamai da uwayen yaran makarantar mata ta Dapchi sun rufe makarantar domin tsoron da suke da shi na kawo sabon hari na ‘yan boko haram.

Makarantar ce aka sace ‘yan mata 104 tare da Leah wadda har yanzu take tsare tun 19 Fabarairun 2018.

Majiya daga makarantar ta ce kungiyar ta rufe makarantar ne saboda umarnin da suka samu daga wurin jami’an tsaro na su kwashe yaran.

Shugaban kungiyar wadanda aka sace yaransu a Dapchi Alhaji Bashir Manzo ya ce JTF Kwamanda ya umarce su da su kwashe yaransu su kai gidan wani basarake suka ga haka ba zai yi wu ba .

Ya ce sun rubutawa jami’an tsaro da ma’aikatar ilmi kan matakin da suka dauka na rufe makarantar.

Sun dauki matakin ne gaba dayansu kan bayanan sirri da suka samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *