‘Yan ta’adda ɗauke da makamai sun yi garkuwa da mutane shidda a ƙauyen Gurin kan iyakar Nijeriya da Kamaru a ƙaramar hukumar Fufore jihar Adamawa.

Mazauna wurin sun byar da bayanin wasu gungun mutane ne ‘yan bindiga suka shiga ƙauyen in da suka tafi da wasu yara su shidda.

Mutanen ƙauyen sun ce yara shidda ne aka sace amma ‘yan sanda sun ce uku ne.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Adamawa DSP Suleiman Nguroje ya ce maharan sun yi garkuwa da mutun hudu a farko amma sun saki ɗaya domin ya kawo labari gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *