An Tir Da Allah Wadai Da Irin Shigar Nuna Tsaraici Da Jarumar Finafinan Hausa, Fati Washa Ta Yi Da Sunan Murnar Samun ‘Yancin Nijeriya.

Mujallar Managarciya ta ci karo da labarai na tsinuwa da gardama kan shigar da jarumar ta yi in da wasu mutane ke ganin laifinta wasu kuma akasin haka.

Jarumar ta yi shigarta yanda take so ta fitar domin burge masoyanta da masu yi mata fatan alheri.

Bayan fitar hotunan sai waɗan da ba ta ɗaura sanwar miyar da su ba suka yi mata caa da kalmomin ɓatanci kanta.

Yakamata mutane bayan sun gama ƙare kallonsu kanta su tsine mata madadin yi mata addu’ar shiriya da tausayawa.

Bai kamata mutane su zama masu addini da tarbiya a baki ba a duk lokacin da suka ga mutum ya aikata abin da baikamata ba sai zagi da tsinuwa amma ba za su yi la’akari da ganin abin da suka yi da kalaman nasu ba addini ba ne son zuciya ne tsagwaronsa.

Fati Washa hotunan nata ba su dace ba a tsarin addini da al’adar malam Bahaushe, amma mafiyawan masu tsinuwa gareta suna iya aikata laifin da yafi nata tun da har suke kallon sun fi ta nagarta bayan kuma suna cin kasuwa ɗaya da ita.

Ba wani mutum da ke nisanta kansa da kaba’ira da kaucewa kallon tsiraici da har zai tsaya kallon hoton Washa har ya ga ashe na tsiraici ne.

Mutanen da ke tsine mata wurin nunawa duniya ita ‘yar iska ce tun da ba su da alaƙa ta jini da ita, ba su gane duniya na kallon sun fita iskancin tun da har suna iya kallon abin da ta yi domin su ko wasunsu su kalla.

Kai mai tsinuwa ka gane ba zaka tsalkake kanka ba da tsinewa ɗan uuwanka musulmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *