Spread the love

An gudanar da daurin auren ‘yar Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da angonta mai shekaru 22 a garin Maradun dake jihar ta Zamfara.


Amarya Rukayyah da angonta Muhtar Ahmed Dan Madami an ɗaura auren a faɗar sarkin Maradun.
Gwamnonin Sokoto, Adamawa,Imo da mataimakin gwamna Borno Jihar sun halarci auren.

Haka kuma Alhaji Sule Lamido, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Ahmed Sani Yarima, Alhaji Attajiru and Alhaji Ibrahim Shehu Shema, duk tsoffin gwamnoni ne na Jigawa, Kano, Zamfara, Sokoto da Katsina.

Shi ma kakakin majalisar jihar Zamfara ya halarta.
Sauran ƴan siyasa sun haɗa da Senata Abdul S. Ningi, Sen. Kabiru Marafa, Sen. Muhammad Magoro, Sen. Lado da Hon. Kawu Sumaila, Hon Bashir Adamu Kazaure, Hon. Muhammad Umara Kumalia and Muhammad Sani Abacha.

An daura auren bayan biyan sadakin dubu 100.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *