Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce matukar ta cika burin kungiyar Kwadago na karin albashi mafi karanci na 30,000 yawan kudin zai kai biliyan 580, lalle hakan zai haifar da korar ma’aikata.

Ministan Kwadago da aikin yi Chris Ngige ya furta haka a birnin Abuja a lokacin da shugabannin hadadiyar kungiyar kwadago takai mashi ziyarar ban girma.

Kungiyar Kwadago a Laraba data gabata ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin sati biyu ta biya bukatunta na karin mafi karancin albashi dubu 30.

Ngige ya ce gwamnati za ta fita batun lamarin da yake tarnaki ga ma’aikata.

Ya roki kungiyar kwadago ta karbi dan karin da za a yi wa ma’aikata masu mataki na 7 zuwa na 17.

Ya kara da cewar wata uku ne gwamnati ta yi ba ta fara biyan sabon karin ba.

Ya ce karin mafi karancin albashin na dubu 30 zai fara ne kan ma’aikata da ke mataki na 1 zuwa na 6, hakan zai taimaki wadan da suke kasa a harkar aikin gwamnati.

Shugaban UCL Joe Ajaero ya yi kira ga hukumomi masu zaman kansu su dubi lamarin karin albashin ga ma’aikatansu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *