Spread the love

Ƙungiyar da aka fi sani da ƙungiyar lauyoyi maras shinge ta zargi sama da kashi 69 na mutanen da ake tsare da su a gidan yarin Nijeriya masu jiran shari’a ne ba waɗanda aka yankewa hukunci ba.

Jagoran ƙungiyar a Nijeriya Angela Uwandu ta faɗi haka a Abuja wurin ƙaddamar da shirin samun ‘yanci ‘safe project’ mai taken ƙarfafa jigogin ƙasa, abin da suke iyawa da danne haƙƙinsu a Nijeriya.

A cewarta ƙungiyarsu za ta bi matakin shari’a ga waɗan da lamarin ya shafa don magance cin zarafin shari’a da walaƙanta waɗanda aka tsare abin da ake zargi jami’an tsaro na yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *