Spread the love

Wasu rahotanni da ke yawo suna nuna akwai ɓaraka a fadar shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya sassauta biyayyarsa ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

A wata mujalla mai suna ‘This is Nigeria’ da aka zagaya da ita a wurin bukin samun ƴancin kai na Nijriya shekara 59 a fadar shugaban ƙasa, Osinbajo ya taya Buhari da matarsa da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu.

A saƙonsa da aka buga a shafi na 15 a bugu na musamman da aka yi akan ‘mataki na gaba na shugaba Buhari’ da majalisa ta 9 da ‘yan Nijeriya dake cikin ƙasa da waje ya kira wannan saƙon ‘biyayyar da ba ta da surki’.

Ya bayyana Buhari amatsayin mai gidansa da yake jin daɗin aiki ƙarƙashinsa ba wani abu da yakamata ya yi kamar yi masa biyaya, ya yi alƙawalin tsayawa tare da shi ya ba da tashi gudunmuwar ciyar da ƙasa gaba a kowane lokaci.

“Ina kira ga mutanen Nijeriya nagari da su goyi bayan Shugaba Buhari a gina ƙasa don ta zama abar tinƙaho” in ji Osinbajo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *