Spread the love

Kotun ɗaukaka ƙara dake Kaduna Ta Ayyana zaɓen Kujerar ɗan Majalisa Mai Waƙiltar ƙaramar Hukumar Isa da Sabon Birni a Matsayin Wanda Bai Kammalaba (Inconclusive)

Kotun Tace Za’a Sake Zaɓen a Mazaɓu Guda (3) kuma ta Umurci Hukumar zaɓe Ta Sake gudanar da zaɓe a Waɗan nan Mazaɓun Cikin Kwana 90

1- Mazaɓar Gebe ‘A’
2- Mazaɓar Gebe ‘B’ da
3- Mazaɓar ‘Yan Fako

Alhaji Bargaja ne na jam’iyar PDP ke saman kujerar yayin da Alhaji Aminu Isa na jam’iyar APC ya ƙalubalance zaɓen da aka ayyana PDP ta samu nasara kansa.

Ya sha kaye Tarabunal ya ɗaukaka ƙara gashi yanzu ya samu nasara abin jira a gani yana iya samun nasara a mazaɓun da za a sake zaɓe domin jam’iyar PDP na da ɗimbin magoya baya a wurin mazaɓar tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa ce.

Yankin nada ɗimbin matsaloli da gwamnatin Sokoto ta ƙyale ba ta yi masu komai ba musamman gadar Bafarawa da ta yanke tsawon lokaci har yanzu ba maganar gyaranta wannan na iya sanya su zaɓi APC da tunanin ɗan majalisar ya yi wani abu a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *