Spread the love

Daga Yusuf Dingyadi, Sokoto.

GABATARWA
A ranar Larba gobe ta 2 ga watan Oktoba na shekarar 2019 Kotun
sauraren kararrakin zaben na gwamna da ta yi zaman ta a jihar Sokoto
karkashin jagorancin Mai shari’a Abbas Bwale zata gabatar da hukunci
dangane da makomar abin da ta kai karshe akansa na sauraren shari’ar
korafi akan sakamakon zaben da aka gudanar na gwamna a jihar Sokoto
wanda Rt. Hon Aminu Waziri Tambuwal ya lashe da yawan kuri’u har 342
akan dan takarar jam’iyyar APC Hon. Ahmed Aliyu Sokoto.
Hukuncin kotun mai lamba EPT/SKT/GOV/01?19 dai za a gabatar dashi a
harabar babba kotun Majistare dake a Wuse, Zone 2 cikin Abuja da
sanyin safiyar ranar larba kuma an tunanin shugaban kotun ne zai
karanta sakamakon abin da suka cimma  na matsayar hukuncinsu.
Kamar sauran hukunci da aka karanta a baya kamin wannan, ana tunanin
duk yadda hukuncin ya kasance ma kowane bangare, akwai yiyuwar daukaka
kara don neman bahasi a gaba akan rashin amicewa da hukuncin bisa
yadda shari’ar da tsarin mulkin kasa suka tanadar.
Don haka anan muhimmin nazari shi ne dangne da yadda ake jin ko gamsuwa ga
lamuran da suka faru tun kamin jiran jin ko wane irin hukunci ne dai
su alkalan kotun ta sauraren shari’ar zasu baiayna ma al’ummar jihar
Sokoto.
Hakika hakan na faruwa a yadda ake ganin tayi zafi har aka kasa
gabatar da hukuncin a ainihin bagiren da aka yi zaman sauraren shari’a
ko aikata abin da ake son gane gaskiyarsa.
Gabatar da hukuncin kotu ko karanta shi a ko’ina cikin Najeriya,
mussaman sabanin inda akayi shari’ar ko sauraren shari’ar yana bisa
ka’ida, muddin babu son kai ko cin zarafin wani bangare, mussaman ma
har idan akwai barazana tsaro ko tunanin iya faruwar wani abu na
tashin hankali ko wani dalili da Alkalan suke ganin bai dace ba ko
yana da hatsari garesu da rayukansu da dukiyoyinsu.
Hausawa kance; iyakar tika-tik don kuwa duk abin da ake kidaya yau da
gobe, hakika zai kai karshe, kuma komi nisan jifa hakika zata fado
kasa. Yanzu kam abin da Sakkwatawa suke jira, kuma askin yazo har
gaban goshi don tabbatar da ‘ware aya daga tsakuwa’ da baiwa mai
gaskiya tabbaci na gaskiya akan abin da su alkalan suka hango ko suke
ganin iya tasu basira shi ne gaskiya
SAURAN ME KUMA?
Alhamudullilah! Yanzu an kai karshe da sanya rana na baiyana da
sauraren hukuncin shari’ar da ta kwashe lokuta tare da daukar hankulan
jama’a dabam dabam a lokuta dabam dabam.
Ranar Larba zata kasance ranar da kotun zata baiyanawa duniya nata
matsayi akan abin da ta ji ko saurare akan makomar alkiblar zaben da ya tabbatar da nasarar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a karo na biyu na
jagorancin jihar Sokoto.
Duk matakin da kotun ta dauka a yanzu akan abin da take hankoron shi ne
dai-dai na hukunci; wannan ba zai kai karshe ga shari’ar ba har sai
dayan bangare da bai jitu da abin da aka zartar ba, yaje gaba a kotun
daukaka kara ko kuma kotun koli wadda ake yiwa lakabi da kotun ‘Allah
Ya isa!’
BAYANIN SHIGA KOTU
Ga bayanin dai na shari’ar shine cewar, dan takarar gwamna na
jam’iyyar APC Hon. Ahmed Aliyu ne ya kalubalanci sakamakon zaben da
hukumar zabe ta Kasa INEC ta bayar na aiyana dan takarar gwamnan jihar
Sokoto na jam’iyyar PDP Rt. Hon Aminu Waziri Tambuwal da cewar shine
ya lashe zaben bayan sake gudanar da zabe a karo na biyu ko kuma abin
da ake kira ‘Inconclusive’
Tashin farkon zaben dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP Rt. Hon Aminu
Waziri Tambuwal ya lashe zaben da rinjayen kuri’u har 3413 don zama
zabbaben gwamna a karo na biyu, sai dai hukumar zabe ta kasa INEc ta
baiyan akwai matsala cewar ba a yi zabe a  wasu rumfuna ba, abin
da ya janyo aka sake gudanar da zaben wanda ya sanya Gwamna Tambuwal
ya samu rinjaye da kuri’u har 342 a karo na biyu.
Kodayake jam’iyyar APC bata musa cewar gwamna Tambuwal ya samu wadanan
kuri’un da rinjaye na farko da na biyu ba, amma tana ganin an tabka
magudi na karin yawan kuri’u a wasu rumfuna ko hana ma magoya bayanta
gudanar da zabe, abuin da lauyoyin jam’iyyar PDP da na INEC suka ki
amincewa dashi a bayanan da suka yiwa kotu.
Hujjarsu ta kin amincewa ma zargin APC na cewar anyi amfani da wasu
hanyoyin hana magoya bayansu yin zabe shine,babu wanda ya san wanene
nashi ko ba nashi ba; har sai an baiyana sakamako a bayan zabe. Don
kuwa, sanin rinjaye ko sanin wanene zai ci zabe a rumfar zabe yana da
matukar wuyar gaske; tamkar mace mai ciki ce, tana iya haihuwa da
namiji ko diya ko tayi bari ko ta mutu da ita da abin da yake a cikin
nata baki daya.

LAMARIN TSARO A SHARI’A
Yunkurin musayar kalamai da neman bata-kashi da hayaniya wadda ta faru
a gaban kotun da harabar ta a lokuta biyu ya sanya jami’an tsaro suka
dauki matakin tsaro mai karfi a duk lokacin da ake sauraren shari’ar
domin baiwa rayuka da dukiyoyin jama’a tsaro ga bata garin da ake
amfani dasu don haddasa tarzoma ko neman tashin hankali.
Sau da yawa Hukumomin tsaro na Yan Sanda da Civil Defence da SSS na
bayar da sanarwa na taka burki akan halartar harabar kotun ga duk mai
neman fitina ko tayar da hankali a tsakanin wasu magoya bayan dukkan
jam’iyyun guda biyu.
Ga alamun da suka nuna dai an gudanar da sauraren shari’ar ta gwamna a
cikin muhimmin matakin tsaro sabanin sauran shari’un da aka gudanar a
cikin ginin babban kotun jiha dake Sokoto.

GABATAR DA SHAIDU DA CHAKWAKIYA
Dukkanin manyan lauyoyin masu gabatar da kara da yin kariya da na INEC
sun gabatar da hujjojinsu akan tsarin mulki da na shari’a da dokokin
zabe na “Electoral act’ dalilansu tare da tabbaci akan abin da suka
sani akan wannan zaben.
Lauyan dan takarar jam’iyyar APC wanda shine mai kara Lauya Alex
Izinwon, SAN ya jagoranci sauran lauyoyin jam’iyyar da na dan takara
wajen gabatar da hujjoji tare da shaidu guda 11 inda suka kawo
bayanai don nuna gaskiyar zargin cewar, tun farko su ne ya dace ache sun
ci zabe, sai hukumar zabe ta INEC taki basu; lauyoyin jam’iyyar APC
din sun ci kasuwa tare da baiyana ma kotu dalilan da suke neman a soke
zabe don basu ko sake wani zabe ko ma ayi zaben cike guraben inda ba
ayi ba don ganin da suke yi na sun cancanta da haka suna da rinjaye.
BAYANIN GASKIYA NA INEC AKAN ‘INCONCLUSIVE’
Wannan ne ya kawo mu akan matakin da babban Lauyan Hukumar Zabe ta
kasa, INEC Barista Alhassan Umar, SAN yayi akan cewar ba zai kawo
shaidu da tun farko yayi niyya ba, saboda kuwa ya tatsi shaidun da
yake so ga shaidun dukkanin jam’iyyun guda biyu.
Lauyan ya tabbatar ma kotu cewar, shi kam ya gamsu da bayanai da ya
samu, don kuwa shaidun sun tabbatar dai anyi zabe, kuma babu wata
hujja mai karfi daga shaidun APC na cewar INEC ta hada kai don yiwa
wata jam’iyya aringizo.
Hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da cewar, tun farko ta bi dukkanin
ka’idodin wadanda shari’a da dokar zabe ta tsara da gindiya mata ga
zaben gaskiya da adalci a lokacin, abin da ya sanya tashin farko taki
ta maince da baiyana sakamako saboda zaben da akayi bai kamalla ba,
wanda APC da kanta ta amince da matakin; duk da irin korafin da PDP
tayi. Wannan ne ya sanya aka gudanar da zabe na ‘inconclusive’ abin da
ya baiwa jam’iyyar PDP galaba akan APC inda ya sanya aka baiyana wanda
ya lashe zabe bisa ka’idar dokar zabe ta kasa da tsarin mulki.
Zaben na karo shine ya tabbatar da baiyana mai rinjaye ba tare da
gardama ko ha’inci ba; haka ma ya nuna maras rinjaye.Sakamakon ya
sanya INEC ta kamalla zabe bisa ka’ida da bin dokar zabe ta kasa.
Hakan ya sanya ta aiyana dan takarar jam’iyayr PDP, Rt. Hon Aminu
Waziri Tambuwal da cewar shine ya wanda ya lashe zaben gwamna bisa
dokokin kasa da hujja ta yawan kuri’un da aka jefa a karo na biyu.
Lauyan Hukumar zabe Alhassan Umar, SAN ya tabbatar ma kotu cewar, babu
wani dalili da zai sanya a zargi hukumar zabe ta INEC da nuna goyon
baya ko daukar wata jam’iyya saman wata, ko aikata wani hali na kauce
ma dokar zabe don biyan bukatar wasu.
Don kuwa INEC ta bi duk hanyoyi da suka dace, bisa ka’ida na kiyaye
hakkin zabe har aka samu wanda ya lashe zabe da wanda ya fadi zabe,
abin da ya bayar da dama gabatar da korafi ga inda aka tsara hakan.
Bayninsa ya nuna cewar; dukkan shaidun da shaidar da suka bayar akan
zargin magudin zabe ko aringizo na kuri’a da cewar jita-jita ce, wadda
babu tabbaci ko makama don hukumar INEC ta san zaben kalau yake a bisa
gaskiya da tsari na dokokin kasa.
Haka ma INEC ta baiyana cewar, baki dayan shaidu na jam’iyyar APC guda
11 babu ko daya daga cikinsu ba wanda ya gani ko akayi dashi, illa
bayani ne na ‘naji’  amma ban gani ba’ ga yin zargin anyi magudin don
wani dan takara. Don kuwa basu da hujja na cewar ga wadanda suka yi ko
wanene aka yiwa magudin.
Bayanin na INEC mai dauke da kwarin guiwa da tabbatar da gaskiyar
tabbacin nasarar PDP alamu ne dake da fatan alheri ga makomar
shari’ar. Don kuwa ba ruwan shari’a da bin jita-jita ko shaidun zur
akan abin da babu tabbaci bai da hujja ko gaskiya akan inda aka ji
shi, a takaice dai babu abin kamawa a cikin bayanin na masu karar.

BAYANIN LAUYAN PDP DA HUJJOJI
Tun farko dai Babban Lauyan PDP dake jagorantar sauran lauyoyi
Emmanuel C Ukala, SAN ya tabbatarwa alkalan kotun cewar; bayani da
shaidun da aka gabatar na jam’iyyar APC babu hujja ko gaskiya garesu,
illa dai an gina su ne akan yaudara da neman cin duga-dugan jam’iyyar
PDP da dan takararta da yayi nasara don biyan wata bukata.
Ya baiyana ma kotu cewar, sam bai dace a saurare sub a, don basu a
bisa tsari sun dogara ga jita-jita da rashin tabbaci tare da neman
bata lokacin kotu da janyo husuma da rashin tabbaci akan abin da Allah
Ya riga yayi ikonsa akai..
Lauyan PDP Barista Ukala, SAN ya nemi kotu da tayi watsi da bayanan na
shaidun APC don kuwa sun kauce ma tsarin mulkin kasa da na dokokin
zabe tare da neman bata lokacin alkalan ga abin da basu gani ko suke
da tabbaci ba.
Yayi mamakin da kusan dukkan bayanin na masu shaidu na jam’iyyar APC
babu wanda ya amince da ya gani ko ya san ko yana anan akayi abin da
yake yiwa shaida ba.
Wadanan bayanan nasu akan hujjojin anyi magudin sun kasa yin bayani
dalla-dalla ina akayi ko su waye ne aka dauki hayarsu har suka aikata
hakan ga tabka magudi don baiwa dan takarar jam’iyyar PDP dama fiye da
na APC.
Jam’iyyar PDP dai ta gabatar da shaidu guda 8 gaban kotu don tabbatar
da bayanin cin zabe a bisa ka’ida da dokar zabe ta kasa.
Bayanin na Lauyan PDP ya tabo yadda tun farko jam’iyyar PDP ta samu
kuri’u masu yawa amma jam’iyyar APC taki ta amince tare da janyo sake
gudanar da zabe a karo na biyu abin da ya haddasa ‘inconclusive’ karo
na farko ga tarihin siyasa da zabe a jihar Sokoto.
Lauyan ya nuna cewar; anyi amfani da wasu hanyoyi ne don ganin an
cimma biyan bukata a tabbatar da PDP bata kai bante ta ba, amma hakan
bai yiyu ba, don kuwa al’ummar jihar Sokoto sun tsaya kai da fata sai
har sun tabbatar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu nasara.
Wannan goyon bayan da jama’a suka nuna ma jam’iyyar PDP da dan
takararta gwamna Waziri Tambuwal ya nuna amincewa da kuma yarda da
suke da garesa na ya samar musu makomar da ta dace ga ciyar da jiharsu
gaba da inganta rayuwarsu bisa tafarki nagari.
Don haka Lauyan PDP tare da sauran lauyoyin sun baiyana ma kotu cewar,
duk hujjojin da suka kawo sun dace da tsari na dokar kasa da dokar
zabe don ganin shari’a ta kara tabbatar da abin da jama’a suka
tabbatar na cewar, Gwamna Tambuwal shine hallatacen zabinsu.
Sakamakon haka ya nemi Alkalan kotu dasu dubi hujjojin gaskiya bisa
dokokin kasa don yin watsi da masu aikin da jita-jita, wadanda suka
dogara kacokan akan neman wani ya rasa don abasu, ba wai don bin doka
da oda na zabe ba; sai kawai don neman samun dalas ga abin da bai
hallata garesu ba.
Wannan bayanin nasa shine abin da ake ganin dacewa ga tabbatar da
cewar, ga inda al’ummar jihar Sokoto suka amincewa ga tabbacin abin da
suka zaba bisa ka’ida tare da ganin sun samar ma makomarsu.Al’ummar jihar Sokoto mutane ne masu kishin jiharsu, don haka duk abin
da zai girgiza zaman lafiya ko ci gabansu hakika abin gudu ne da
damuwa, don haka samar da zaman lafiya da ci gaba shine kalubale ga
kowane dan jihar Sokoto na gari.

Daga
Yusuf Dingyadi, Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *