Spread the love

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni zai yi amfani da karfin da kwallo take da shi ya samarwa matasan jihar masu sha’awar kwallon kafar aikin yi.

Babban Darakta a hukumar wasanni ta jihar Yobe Dakta Abubakar Ago ya sanarwa manema labarai cewa gwamanan jiha ya aminta da biyan alawus na fiye da matasan ‘yan kwallon kafa 70.

Ya ce ‘yan wasan da aka zabo da masu horar da su za a basu takardar soma aiki da alawus na su na wata daga ranar Alhamis, wannan yana faruwa ne kan yanda gwamna ke son tallafawa matasa

Ago ya yi bayanin wadanda za su ci gajiyar ‘yan wasa 25 daga karamar kungiyar wasa ta Yobe(Desert star), sai 30 ‘yan kasa da shekara 15, da masu horaswa 15 da wasu ma’aikata biyu.

Wannan hobbasa wani bangare ne na alkawalin da gwamna ya yi na zai samar wa matasa aikin yi, wannan abin zai kara inganta harkar kwallon kafa a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *