Spread the love

Mutum goma sha hudu ne suka rasu bayan sun ci abinci mai guba a kauyen Moda cikin karamar hukumar Anka a jihar Zamfara

Mutanen garin sun gayawa jaridar daily trust cewa matar gidan ce ta zuba gishirin lalle a cikin miyar abincin daren gidan ba tare da ta sani ba ta zuba magin Ajino moto tare da gishirin lalle wuri guda, sannan ta zuba a miya ta burkake ciki.

“Duk wanda ya ci abincin nan sai da ya mutu, takwas daga cikinsu sun rasu a asibiti, shida kuma sun bar Duniya a gidajensu.” kamar yadda wani mutum ya labarta lamarin.

Mutum takwas daga cikin mutanen ‘yan dangi daya ne, duk wanda yasan al’adar Bahaushe yasan da dare in aka kammala abinci ana fitowa da shi waje duk mai bukata makwabta da kowa ya zo ya ci.

Abin tausayi duk mutanen da suka ci abincin nan sun mutu har matar da ta dafa abincin da wasu mata hudu.

Abokiyar zaman matar da mijinta sun tsalke kaddarar domin a lokacin da aka kammala abincin ba su nan, wadan da suka rasu an yi masu jana’iza an binne su kamar yadda shari’a ta tanadar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, amma shi ya ce mutun takwas suka rasu. Ya ce suna kan binciken lamarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *