‘Yan Bindiga Sun Sace Wata Sabuwar Amarya A Hanyarta Ta Zuwa Sokoto

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga da ake zatton masu garkuwa da mutane ne sun sace wata Halimatu Abdullahi Bunun Bela.

A cewar rahotannin, anyi garkuwa da Halima wacce ta kasance sabuwar amarya a hanyarta ta zuwa jihar Sokoto daga Kauran Namoda dake jihar Zamfara.

Hakazalika wani mai amfani da shafin sadarwa ta Facebook, Honarabul Dayyabu Mande Tsafe ya wallafa labarin a shafinsa, inda ya rubuta.

“Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un, masu garkuwa da mutane sunyi garkuwa da kanwata Halimatu Bunun Bela. Allah yai maki mafita.”

Harkar masu garkuwa da mutane a jihohin Zamfara da Sokoto na da ɗaure kai duk da an samu raguwar lamarin a Zamfara.

Jihar Sokoto abin sai ƙarin addu’a yanda ake ta fama sace mutane a jihar.

Kwananan ma an yi garkuwa da wani hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Tukur Sabaru bayan ɗauki ɗaya ɗaya da ake yi wa mutane a ƙauyukkan Tureta da Sabon Birni.

Akwai bukatar gwamnati ta ƙara tashi tsaye ga harkar tsaron mutane da dukiyoyinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *