Spread the love

BAYAN SHEKARA 59 DA SAMUN INCIN KAI HAR YANZU NAGERIYA CIKE TAKE DA TARIN MATSALOLI

Ya kamata mu tambayi kawunan mu akan Shin haka muke so ace Wannan ƙasa (ta Nijeriya) ta kasance?

Shin Zamu Iya Samun Mutum miliyan biyu da Za su amsa Mana da “Eh”? Akan haka muke so muga Wannan kasar?

Wannan Tambaya ce da na Rasa Amsarta, Kamar yadda Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya Bayyana a Taron cikar Nageriyabe 59 da Samun Incin Kai da akayi a Babban masallachin Abuja a Ranar jumu’ar da ta gabata.

A daidai Wannan Gaɓar ne Sarkin Musulmi ya buƙaci Muhammadu Buhari da sauran ‘yan Siyasa da su amsa Masa Wannan Tambayar ta hannun Ministan Abuja Muhammad Musa Bello Wanda Shi ne Ya waƙilci Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Taron.

Har wayau Sarkin Musulmi Ya Kara da Cewa, Gwamnati ba ta Mutum ɗaya ba ce kawai, tamuce da ya kamata mu hada Kai domin mu ciyarda kasarnan gaba, a Matsayin mu na Musulmi munsan muhimmanchin Shugabanci don haka ba za mu ji kunyar Tambayar Shuwagabanni ba akan Ya kamata su tsaya su yi wa wayanda suke mulka adalci.

Har ila Yau Sarkin Musulmi Ya nuna Gazawar Gwamnati na Kasa samarwa Matasa aikin yi Wanda Hakan ke Sanya su gudun hijira Suna zuwa ƙasashen turai har Ana kashinsu a Wasu wurare.

Haka Kuma ya buƙaci Shuwagabanni su Samarda hanyoyin wadata Al’umma Wanda zai Sanya ‘yan Nageriya Barin fita waje domin neman aikinyi Wanda Saboda Wannan Dalilin ne aka zaɓe su.

“Matasanmu dole ne su Zama abin alfahari, ko an ƙi ko an so, Matasan mu Suna da baiwa da Yawa Wacce Za su iya sarrafata a ko ina, Kuma Ayi alfahari dasu, Amma Yau Wasu daga cikin waɗannan Matasa sun Faɗa harkar miyagun laifukka, don haka ya Zama dole mu binciko mi ke haifar da haka domin Samun Mafita.” Kamar Yanda ya Faɗa.

Haka har wayau Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya buƙaci aƙara Faɗaɗa Gina makarantu a Arewacin Nageriya domin akwai akalla Matasa miliyan 10 dake Yawon bara Alhali Musulunci ya Hana.

“Wane Mataki Gwamnati ta ɗauka?, Akwai Wani tsari da tsohuwar gwamnatin Da ta gabata ta Gudluck Jonathan ta fito da shi na Gina makarantun almajirai a duk fadin kasarnan, me ya faru da Wannan Tsarin? Yana da Matukar muhimmanci Gwamnati ta binciko domin ta ci gaba da Wannan Tsarin domin zai taimaka wajen rage matsaloli bara dake addabarmu”.

Managarciya ta samu waɗannan kalamai ne a wani bayani da mai baiwa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin sadarwa na zamani Jamilu Sani Rarah Sokoto ya fitar.

Jawaban ƙarara sun fito da hange da shawarar Sarkin musulmi kan makomar ƙasar nan saura da mi a yi amfani da shawararsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *