Spread the love

Daga Aliyu Ahmad.

Fitaccen mai kama barayin shanu, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata ayyukan ta’addanci a fadin ƙasar nan, Alhaji Shehu Musa, wanda ake yi wa laƙabin Shehu Aljan ya nuna rashin goyon bayansa ga sulhun da wasu gwamnoni suke yi da ‘yan ta’adda musamman na yankunan Arewa.

Shehu Aljan, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a makon da ya gabata a garin Kano, bayan nasarar kama wasu ɓarayin shanu tare da ƙwato dubban shanu da makamai daga wajen su a dajin Falgore dake ƙaramar hukumar Tudun Wada a jihar Kano, ya kuma ƙara da cewa a shirya yake da duk wani tsageran ɗan ta’adda da yake ji da kansa.

A yayin da yake ƙarin haske kan yadda aka yi suka yi nasara akan barayin shanun, ya ce sun ɗauki ‘yan kwanaki suna artabu da ɓarayin, daga bisani Allah ya ba su sa’a suka kama da yawa daga cikin ɓarayin, tare da ƙwato shanu sama da dubu biyu da kuma makamai da kayan sojoji a wurin su.

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta nuna matuƙar farin cikin ta game da nasarar kama ɓarayin shanun da Shehu Aljan ya yi, inda ta bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga gwamnatin sa da ma al’ummar jihar Kano baki ɗaya, wanda kuma tarihin jihar ba zai mance da hakan ba.

Sannan kuma Gwamna Ganduje da kansa tare da rakiyar kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ne suka jagoranci mika shanun ga masu shi tare kuma da gurfanar da ɓarayin.

Game da batun zaman sulhu da wasu gwamnoni suke yi da ‘yan ta’adda kuma, musamman masu garkuwa da mutane, Aljan ya nuna rashin goyon bayan sa game da hakan, inda ya kawo hujja da cewa sau da yawa idan an yi sulhun makaman da tubabbun ‘yan ta’addan suke kawowa ba su taka kara sun karya ba.

“A lokacin da barayin suke kawo farmaki garuruwan mutane, za ka gan su su sama da dari biyar zuwa dubu daya a babura kuma kowanne su xauke da bindiga, amma da zarar an ce an yi sulhu, sai ka ga sun kawo bindigun da ba su wuce uku ko biyar ba. To sauran makaman ina suke? Ka ga kenan da sauran rina a kaba”, inji Shehu Aljan.

Aljan ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa akwai bukatar ya zauna da gwamnonin da suke cewa za su sulhunta da ‘yan ta’adda, domin a fahimtar sa idan har za a dinga zaman sulhu da varayin, me zai sa kuma ana narkar da kuɗi da sunan tsaro. Saboda duk gwamnan da zai yi sulhu da ‘yan ta’adda babu maganar a ce ana ware wasu kudade na musamman da sunan samar da tsaro. Tunda ba varayin ake baiwa kudin ba.

Sakamakon irin nasarar da Shehu Aljan ke samu kan ‘yan ta’addan, ya nemi gwamnati ta ci gaba da ba shi dama domin ci gaba da yakar ‘yan ta’adda musamman masu garkuwa da mutane a duk inda suke a fadin kasar nan.

Ya ce a matsayin sa na shugaban sashen tsaro na Kungiyar Miyetti Allah, kuma masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba za su zuba ido tsaro ya tabarbare a kasar nan ba ba tare da sun bayar da gudummawar su wajen ganin an samu ingantaccen tsaro a kasar nan. Wanda kuma ba wanda zai saka musu da abinda suke yi saidai Allah.

Shehu Aljan ya kuma ja kunnen ‘yan ta’adda cewa kada su bari ya yi ido hudu da su, domin ba za su ji da dadi ba. Kuma ba zai yi kira gare su da su tuba ba.

“Idan ka duba a cikin kwanaki hudu muka yi nasarar kama barayin shanun Kano. Ka ga idan sauran gwamnoni musamman na yankin Arewa da suke fama da matsalar ‘yan ta’adda za su bayar da hadin kai kamar yadda Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje ya bayar, da tuntuni an toshe barakar da ake samu a fannin tsaro.

“Don haka ina kira da duk wani gwamna da ya yi koyi da Ganduje wajen yakar ta’addanci domin tabbatar da tsaro a jiharsa. Saboda Ganduje ya haxa kai da jami’an tsaro waxanda suka hada da ‘yan sanda, sojoji, ‘yan bangan sa kai, inda ake aiki ba dare da ba rana a birni da kauyukan Kano”.

Jarumi Aljan ya kuma ce tsakaninsa da jami’an tsaron da yake fita aiki da su akwai kyakkyawar fahimta sosai domin suna ba shi hadin kai yadda ya kamata, wanda ba za ma ka iya bambace tsakanin su ba.

Shehu Aljan, wanda ya haura sama da shekara ashirin yana harkar kama barayi, ya bayyana cewa ya yi nasarori da dama a fannin kama barayi, wanda ba za su iya lissafuwa ba, domin ya kama barayi a jihohi irin su Kogi, Neja, Taraba, Katsina, Abuja, Nasarawa, Filato Bauchi da sauransu. Inda kuma a yanzu yake bakin aiki a Kano, kuma ya sha alwashin sai ya ga bayan barayin shanu da masu garkuwa da mutane da sauran ‘yan ta’addan dake Kano.

Saidai a yayin tambayar da aka yi wa Aljan kan ko zai dinga yawo ne jiha-jiha domi yakar ‘yan ta’adda, ya bayyana cewa ba zai shiga kowace jiha ba ba tare da gwamnan jihar ya ba shi goron gayyata ba, kuma koda gwamnan ya neme shi zai gaya masa cewa babu batun yin sulhu da ‘yan ta’addan.

“Duk wani gwamnan da ya san cewa yana fama da ‘yan ta’adda a jihar sa, ban ce ya ba ni ko kobo ba, kawai ya gaya min sunayen yankunan da ake dama da ‘yan ta’addan ya gani ko zai sake jin duriyarsu. Wallahi ba zai sake ji ba”, inji Aljan.

Saidai Aljan ya kara da cewa yana da sharruda biyu zuwa uku da zai gindayawa duk wani gwamna da ya gayyace shi domin kawar masa da ‘yan ta’adda a jiharsa, na farko shine ya zamana cewa idan aka nuna masa inda zai yi aikin, to a zura masa ido kawai. Sannan ba ya buqatar ‘yan katsalandan, ma’ana wadanda da zarar an kamo hanyar nasara a aikin, za su nemi a dakatar, wanda irin wadannan mutanen ba ka rasa suna da hannu a harkar ta’addanci dake aukuwa a jihohinsu.

Game da ko me yake haifar da matsalolin harkar ta’addanci a yankin Arewa, Aljan ya kara da cewa abin mamaki ne yau a mayar da mutanen arewa tamkar wasu raguna, inda za a sace mutum sai an biya kudi kafin a dawo da shi. Kuma kudi mai yawa ba kaxan ba.

“Kudin fansar da ake bayarwa idan an sace mutum shi yake dada jawowa harkar garkuwa da mutane ke kara tasiri, amma idan za su sace a kyale su, dole su sako mutum idan har kwanan sa bai kare ba”, cewarsa.

Shehu Aljan ya kuma qara da jaddada cewa Gwamnoni su daina yin sulhu da ‘yan ta’adda domin yin hakan kuskure ne, a bari su za su yi maganin su, domin babu barau sai bararre.

“Ni da barayin shanu, masu garkuwa da mutane da sauran ‘yan ta’adda, dan-halak-ka-fasa”, cewar Shehu Aljan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *