Spread the love

Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi.

Jihar Kebbi, jiha ce da Allah ya albarkata da ƙasar noma iri daban-daban kama tun daga noman gero, dawa, masara da kuma wake. Sauran sun haɗa da rogo, tumatur, dankali, shinkafa, alkama, waken soya da kuma albasa da sauransu.

Wanda a halin yanzu a jihar ta Kebbi ba a maganar cewa mutun nawa ke noma a jihar ta Kebbi ke yi ba, saboda kusan kashi tamanin da biyar na mutanen jihar ta Kebbi manoma ne da ke noma irin daban- daban a kowane yankin na cikin Jihar, inda suke noma mai yawan gaske da ya sa sunan Jihar ta Kebbi ya kai ko’ina a cikin ƙasar Nijeriya, kai har ma da wasu ƙashashen waje. amma kuma Gwamnatin jihar da ta tarayya sun fi ba da muhimmanci ga noman shinkafa, alkama da kuma waken soya da kiyon kifi, har ila yau dai kuma duk da tallafin da aka bai wa noman shinkafa da alkama a jihar ta Kebbi, bai sa suka fi manoman albasa tasiri musamman wurin samun kayan amfinin gona da kuma sayar da su a cikin duniya ba Domin idan lokacin girbe albasa ya yi ƙaramar hukumar mulki ta Aliero za ta koma kamar kasuwar ƙasashen duniya ta albasa.

Don haka tarihi da masana kan harakar noman albasa sun nuna cewa, an yi watsi da albarkatun aikin noman albasa da ake yi Nijeriya a shekarun baya da suka shuɗe, kuma ana ɗaukar aikin noman na albasa ne kawai don mutane matalauta a Arewacin ƙasar nan kawai ne ke aikin noman albasa, Amman duk da haka noman albasa yana tallafa wa miliyoyin rayukan mutane a Nijeriya da kuma duniya baki ɗaya! A haƙiƙa akwai iyalai da yawa a arewacin jahohin Nijeriya da ke dogara da albarkatun noman Albasa kamar na ƙaramar hukumar mulki ta Aliero a Jihar Kebbi da ma sauran wasu jahohin ƙasar nan, kuma suna rayuwa ne ba tare da sauran mutane ba ko kuma dogaro ga Gwamnatin.

Kayan amfanin gona na Albasa yana da matuƙar muhimmanci ga wasu al’umma, waɗanda sun ɗauke shi a matsayin kasuwanci wanda za su iya dogaro da shi a matsayar wata hanya ta rayuwa, wasu mutanen garin na Aliero ko bayan aikin noman albasa da suka yi kuma sukan sayi albasar domin su sayar. Sayar da albasar da ma shuka ta wannan yana faruwa a al’ummomin Aliero da ma sauran wasu jahohi a cikin ƙasar nan.

Al’adun noma ba shi da wahala kamar yadda za a iya girma a cikin gidan idan mutum na da sha’arwar noman albasa domin yana iya tsira kamar yadda abin da mutane da yawa suka yi tsammanin za a iya dasa shi ne kawai a cikin arewacin Nijeriya. Albasa za a iya shuka ta a kuma girmar da ita a ko’ina cikin wannan ƙasa ta Nijeriya baki ɗaya.

Kasuwancin albasa yana da kyau amma dai yawancin mutane na ganin albasa a matsayin ɗaya daga cikin abincin da muke amfani da ita wurin dafa abinci, amma hakan ya wuce, domin idan mun fahimci cewa za a iya samar da miliyoyin Naira ta hanyar shiga aikin noman albasa a ƙasar mu Nijeriya.

Ga waɗanda ke sha’awar wannan babban kasuwancin noman albasa ya kamata su sauko zuwa yankin ƙaramar hukumar mulki ta Aliero a jihar Kebbi don samun ilimi da basira a kan yadda za a shuka da noman albasa , za mu yi farin ciki don ba ku wasu ƙwararu kan noman albasa masu horaswa game da yadda za ku shiga kasuwancin sayar da albasa da kuma noman ta. Domin Fara noman albasa da kuma kasuwancin ta da kuma cin amfaninta fiye da shuka shinkafa ko alkama. A halin yanzu dai Gwamnatin tarayya da ma ta jahohin ƙasar nan sun karkata akalar tunaninsu ne wurin noman shinkafa da alkama da kuma kiyon kifi kawai, ba tare da waiwaye kan tunanin cewa shi ma noman albasa wata hanya ce ta bunƙasa tattalin arziki al’umma a ƙasar nan ba. Wanda a halin yanzu manoman albasa na garin Aliero da ma garin Yauri binciken da wasu masana da kuma wasu cibiyoyin bincike na wasu jami’o ‘in ƙasar nan da ma na ƙasashen waje da kuma wanda jaridar Leadership A Yau ta gunadar a cikin wannan makon da muke ciki yanu na cewa, manomin albasa yana kusan zama ɗaya da manomin shinkafa a jihar ta Kebbi kan arziki da wadata ta hanyar noma amfanin gona a jihar Kebbi da ma sauran wasu jahohin da ke noman albasa a ƙasar nan ta Nijeriya.

Noman albasa dai sannin kowa ne cewa akwai iraruwan albasa har kala biyu wanda farko akwai gajeren rana da kuma akwai tsawon rana domin albasar tana da bambancin lokaci wurin shuka ta da cirewa.

Manoman albasa na ci gaba da girma a cikin ƙasar Nijeriya musamma a jihar ta Kebbi kamar yadda noman shinkafa ke ta bunƙasa ta hanyar saye da saya wa da kuma shuka ta a gonaki tamkar Shinkafa , ya sa manoma na ƙara wadata da kuma bunƙasa kan amfanin noman albasa. Mafi kyawon sarari na shuka albasa shi ne yawanci 1/2 inci ba ya da zurfin 3/8. Ana sanya layuka mafi kyau a 15 inci dabam- dabam.

Albasa na buƙatar ruwa mai yawa a farkon mataki, don haka idan ba ruwan sama isassu sai a shirya a shayar da ita akai-akai don kyakkyawar riƙewar ruwa. Komawa yana da mahimmanci saboda zai taimaka wa amfanin gona don amfani da kayan gina jiki a cikin ƙasa maimakon raba shi tare da karkare haki kamar yadda aka gano Albasa don yin mafi kyau wanda babu sauran ciyawa.

Bayan bayanan da masana kan noman albasa suka yi a kan ilimin noman albasa da kuma muhinmancinta, wakilin Leadership A Yau da ke Birnin Kebbi ya zagaya fadamar gonakin noman albasa a ƙaramar hukumar. mulki ta Aliero a jihar ta Kebbi domin jin ta bakin manoman albasa a yakin, kuma a cikin zagayen da ya yi ya samu zantawa da manoman albasa da kuma wasu shuwagabanin ƙungiyarr manoman albasa da kuma sayar da ita a kasuwar albasa ta Aliero ga kuma abin da suke cewa .

Ɗaya daga cikin manyan manomin albasa wanda yana noman kimanin buhu 350 zuwa buhu 500 a kowa ce shekara a garin na Aliero mai suna Alhaji Garba Dangaladiman sabon gari Aliero, ya bayyana cewa, noman albasa yana da matuƙar fa’ida musamman ga mutanen garin Aliero, domin ba su da abin da ya fi noman albasa daraja gare su, sobada mafi yawanci mutanen garin na Aliero sun gaji wannan sana’ar noma ga kakanin su ba ko ga uwaye kawai ba, “sannan noman albasa da shi ne mun ka dogara ba mu da wata Sana’a da ta kai sana’ar noman albasa.

Har ilayau ya ci gaba da cewa shi ya fi shekaru hamsin da haihuwa amma duk lalurorin da aka yi mashi a lokacin da yana ƙarami da kuɗin albasa ne, kai ko auren da ya yi duk da kuɗin albasa ne. Ya ce kuma ya gina gidaje da kuɗi albasa. Ya je hajji y-a kuma biya wa wasu duk a cikin arzikin noman albasa. “Kuma wannan bayanin da na ke ba ka tun tashina cikin noman albasa nake har inda nake yanzu”.

Ya ƙara da cewa sukan shuka irin albasa ne kimanin sati uku zuwa huɗu kafi a fara cirewa sai ka shuka shi a gonarka ko ka sayar ga mutanen da ke so. Kuma ya ce, noman albasa yana buƙatar taki na gida da na zamani domin haɗa shi guri ɗaya sai a zuba shi ga albasar da aka riga aka shuka.

Ya ci gaba da cewa, irin albasa kala biyu ne. Akwai farin iri da kuma Jan iri wanda su a garin Aliero sun fi amfani da Jan irin albasa domin ya fi amfani sosai kuma fiye da shekaru hamsin da biyar shi ne manoman albasa a garin Aliero ke amfani da shi wanda tun lokacin ba su taɓa samun wata mastala ba . Ya ce, albasa kwanaki tamani ko kwanaki ɗari za ta yi kafin a girbe ta zuwa kasuwa ko gida. Kamu ya ce, sau ɗaya ake noman albasa. “Ina iya sayar da albasa ta Naira Miliyan biyar zuwa Miliyan goma a shekara, wanda ko a cikin wannan shekara na biya wa mutun uku kujerun hajji na bana wanda kuɗin sun kai kimanin Naira Miliyan uku da ‘yan kai”.

Hakazalika ya ce, tun da ya fara noman albasa kimanin shekara hamsin bai taɓa samun tallafin Gwamnatin ko wani kamfani kan bunƙasa harakar noman albasa ba. Ya ci gaba da cewa lokacin tsohuwar Gwamnatin Sanata Muhammad Adamu Aliero shekaru goma sha biyu da suka gabata an yi musu alkawalin yin kasuwar albasa ta ƙasashen Afirka ta Yamma a garin Aliero wanda yanzu haka wurin na nan a kan hanyar Kata zuwa a garin Jega a kusa da garin Ɗawarai da ke cikin ƙaramar hukumar mulki ta Aliero a jihar ta Kebbi. Saboda haka muna kira ga Gwamnatin tarayya da kuma ta jiha da su bunƙasa aikin noman albasa a jihar ta Kebbi , domin a halin yanzu ƙididiga ta nuna cewa a kasuwar albasa ta ƙasashen Afirka ta Yamma, albasar da ake nomawa a jihar Kebbi ta fi yawa a kasuwar

Shi ma wani noman mai suna Habibu Abdullahi ya bayyana cewa, ya gaji noman albasa ga uwayensa, “Wanda tun da na tashi na tarar da ana noman albasa a gidanmu kuma duka yaran da aka haifa da kuɗin albasa aka raɗa musu suna, haka na tashi na kama noman albasa wanda yanzu a kan noman albasa na dogara da shi.”

Har ila yau ya ci gaba da cewa, a duk shekara yana noma buhun albasa ɗari biyu da hamsin zuwa buhu ɗari uku da hamsin wanda kowane buhu ana sayar da shi kan kudi Naira dubu ashirin zuwa dubu arba’in a kasuwar albasa ta garin na Aliero. Ya ƙara da cewa a kowa ce shekara yana sumun kuɗi ga noman albasa da suka kai kimanin Naira Miliyan huɗu zuwa shida a duk shekara. Hakazalika ya ce, suna neman Gwamnatin da ta taimaka musu kan gina musu wuraren ajiyar albasa domin kauce wa lalacewarta da kuma inganta ta. Ya ce, ‘yan kasuwa daga jahohin Legas, Kalaba, Anambara, Oyo, Enugu, Ebonyi da kuma Neja. Sauran sun haɗa da ƙasashen waje kamar Nijar, Jamhuriyar Benin, Ghana, Mali da kuma Kamaru da ma sauran wasu ƙasashen a cikin ƙasashen Afirka ta Yamma, duka suna zuwa kasuwar garin Aliero kan sayen albasa.

Daga nan ya ƙara da cewa, suna buƙatar kamfunan da za su iya sayen albasa domin sarrafa ta . Hakazalika ya ci gaba da cewa, Gwamnatin jihar ta Kebbi a Ƙarƙashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ba da kwangilar Gina wata katafariya kasuwar albasa a garin na Aliero wadda za ta lashe miliyoyi Nairori wand yanzu haka aikin kasuwar ya yi nisa da nufi cewa akwai alamun ko wata huɓasa kan bunƙasa aikin noman albasa da manoman Kansu.

Shima wani daga cikin shugabanin kasuwar albasa na garin na Aliero kuma manomin ita albasar Alhaji Umaru Sanda Aliero ya bayyana cewa yana yin kasuwar albasa a garin Aliero sai hamdala ga Allah saboda sukan noman albasa da sayar da ita komi sun samun kan ita albasa, “Domin na gina gida na sayi motoci na tafi hajji kuma na biya ma wasu. Kuma a halin yanzu ban da wata Sana’a da ta fi mani noman albasa ko sayar da ita a kasuwa”. Ya ci gaba da cewa: “Akwai wani abin takaici da ban mamaki, fiye da shekara hamsin da biyar mutanen garin Aliero ke noman albasa amma ba’a taɓa samun wata Gwamnatin da ta ce za ta tallafa wa manoman albasa ba ,wanda kuma idan ka duba ko ka kimanta tsakanin noman shinkafa da albasa za ka ga mun fi manoman shinkafa samun arziki noma, domin mu da kuɗaɗen mu ne muke amfani da shi wurin yin aikin noman albasa ba tare da wani tallafin Gwamnati ko wani kamfuni ba , amma manoman shinkafa na tare da bashin da aka ba su tun shekaru biyu da suka gabata, wanda har yanzu wasu manoman shinkafarar ba su iya biya ba. Duk manomin albasa a garin Aliero yana da jarin da zai iya noman da shi, amma abin da manoman albasa ke so a halin yanzu shi ne a tallafa musu ta yadda za su iya yin noma na zamani da kuma kayan aikin noman albasa na zamani. Kana ya ci gaba da cewa Gwamnatin jihar ko ta tarayya su yi tunanin yin haɗin guiwa tsakaninsu da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma domin gina kasuwar albasa ta duniya a cikin jihar ta Kebbi ko da ba cikin garin Aliero ba, amma duk da jihar Kebbi na da iyaka da wasu ƙasashen kamar ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar da kuma Jamhuriyar Benin ka ga ko ana iya yin ita wannan kasuwar ɗaya daga cikin iyakokin nan, wanda yin hakan za ya samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasashen da kuma jahohinsu ya kuma ƙara bunƙasa yanayin kasuwanci a tsakanin ƙasashen”.

Har ila yau ya ce, yana kai albasa daga garin Aliero zuwa kasuwar Ghana da Mali kuma in sayar da ita dadaraja. ‘Haka kuma ina ɗaya daga cikin mutanen da tsohuwar Gwamnatin Sai’du Ɗakin gari ta tura mu zuwa ƙasar Morocco domin harakar noman albasa amma babu kamfani ɗaya da ke sarrafa albasa, sai dai noman wanda mu a garin Aliero mun fi su iya noman ta”. Daga nan ya ci gaba da kira ga Gwamnatin da kuma masu ruwa da tsaki na cikin jihar da ma tarayya da su taimaka wa manoman albasa na garin Aliero domin duk jahohin ƙasar Nijeriya su san cewa garin Aliero a jihar ta Kebbi ta fi kowa noman albasa kai ko ƙasashen afirka ta Yamma sun tabbatar da cewa albasar Aliero ta fi yawa a kasuwar ta ƙasashen na afrika.

Har ila yau shi ma wani ɗan ƙungiyarr manoman albasa da kuma sayar da ita a kasuwar Aliero kuma shi ne mai kula kuɗin shiga na ƙungiyar ta ‘yan albasa na garin Aliero mai suna Alhaji Salihu Hali Aliero ya ce, “Babu shakka albasa garin Aliero ta fi kowance jihar a Nijeriya noman albasa, kuma a kasuwar afirka ta Yamma Albasar Aliero ta fi yawa a kasuwar domin muna kai ta a mota da kuma ta jirgin ruwa zuwa Ghana, Mali, Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin da kuma sauran ƙasashen waje.” Ya ci gaba da cewa: “amma fiye da shekaru hamsin da biyu zuwa da uku muna noman albasa da sayar da ita, Gwamnatin ko wasu kamfuna ba sutaɓa ba mu tallafin noma ba”.

Hakazalika Alhaji Salihu ya yi kira Gwamnatin tarayya da ta taimaka wa mutanen garin Aliero da noman albasa na jihar Kebbi da yi musu kasuwar albasa ta afirika a cikin jihar ta Kebbi domin ƙara bunƙasa aikin noman albasa a jihar Kebbi da kuma ƙasar Nijeriya baki ɗaya. Wanda yin hakan zai samar da kuɗaɗen shiga ga jahohin da tarayya baki ɗaya. Saboda irin kiraye-kirayen da jama’ar garin na Aliero keyi kan bunƙasa harakar noman albasa, Gwamnatin jihar ta Kebbi a Ƙarƙashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta ba da kwangilar gina katafariyar kasuwar albasa da kuma tashar mota a cikin garin na Aliero wadda za ta lashe miliyan Nairori kan gina ta, domin ƙarama manoman albasar ƙwarin guiwa kan bunƙasa aikin noman albasa a jihar.

Har ilaya Gwamnan jihar ta Kebbi kimanin wata biyu da suka gabata ya ziyarci garin na Aliero domin ganawa da manoman albasa da kuma ‘yan kasuwar albasa, inda Gwamnatin Kebbi ta bayyana kudurin ta na gina kasuwar albasar ta Aliero , kuma ga abin da yake cewa “

Gwamnatin Jihar Kebbi a ranar Litinin ta makon da ya gabata tace za ta gina kasuwar albarkatun kayan aikin na albasa a yankin Aliero a jihar.

Gwamna Atiku Bagudu, ya ci gaba da cewa ya yi alkawarin gina kasuwar albasa a garin na Aliero a yayin ziyara a garin na Aliero ranar Litinin ta makon da gabata. Wanda a cikin jawabinsa ga manoma da ‘yan kasuwar albasa a Aliero, ya yi alkawarin cewa za a gina kasuwa a yankin”. Inda a halin yanzu ginar kasuwar yana ci gaba.

Shi ma Sarkin albasa na garin Aliero, Alhaji Bello Uba Aliero wanda Alhaji Aminu Uba Aliero ya wakilta ya ce, duk abin da ake samu na arzikin amfanin noman albasa mutanen garin Aliero sun samu. Amma a halin yanzu babban abin da manoman albasa na jihar Kebbi ke so shi ne a ba su tallafi da kuma samun kamfunan da za su iya sarrafa albasa, sai kuma Gwamnan jihar da tarayya su shigo ciki domin samar wa manoman albasa kayan aikin zamani na noman albasa.

Hakazalika ya ci gaba da cewa mutanen garin Aliero masu noman albasa sun gina gidaje, sun sayi motoci da kuma zuwa hajji. Saboda haka “muna kira ga Gwamnatin da masu ruwa da tsaki na jihar da tarayya da su shigo cikin ƙaramar hukumar mulki ta Aliero domin taimaka wa noman albasa na jihar ta Kebbi kan yadda za su iya noman albasa na zamani. Daga nan ya ce, mutanen garin Aliero na buƙatar horas wa kan yadda ake noman albasa na zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *