Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta tabbatar da samun nasarar cabke Salisu Idiris dan shekara 25, wanda ake zargin ya cinnawa gida wuta wanda haka ya yi sanaddiyar mutuwar iyali uku dake cikin gidan.

Lamarin wanda ya faru a ranar Laraba data gabata a Unguwar Gayawa Tsohuwa karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da sun kama matashin, ya ce wadanda suka kone a gidan da ya sanya wa wuta sun hada da Uba da Uwa da diyarsu ‘yar shekara biyu.

Ya ce ‘yan sanda sun samu labarin sanya wutar sai suka yi amfani da dubarunsu ta hanyar ‘yan sandan ciki domin gano wanda ya yi wannan aika-aikar, sun gano kuma suka kama Salisu na Gayawa Gabas da wasu miki a jikinsa, sun gano ya yi mugun aikin ne tare da wasu mutum biyu da wasu kuma da za a fadada bincike.

A zantawarsa da manema labarai wanda ake zargin yana sana’ar wayar hannu a kasuwar Farm Centre ya aminta da laifinsa ya ce hayarsa aka dauka da alkawalin za a ba shi dubu 200.

Shi kuma ya yarda ne domin yana son kudin ya yi karatun jami’a da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *